Minista Ya Fara Ganawa da Matasa, Nyesom Wike Zai Dakile Zanga Zanga a Abuja

Minista Ya Fara Ganawa da Matasa, Nyesom Wike Zai Dakile Zanga Zanga a Abuja

  • Yayin da ya rage kwanaki biyu a tsunduma zanga-zanga a fadin kasar nan, gwamnati ta fara daukar matakin dakile shi a Abuja
  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce matasa su ne ginshikin birnin kuma bai kamata su yi zanga-zanga ba
  • Tun bayan da yan kasa su ka ayyana aniyar gudanar da zanga-zanga ta kwanaki 10 ne gwamnati ke kokarin dakile haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce su na tattaunawa da matasa domin dakile gudanar da zanga-zanga a babban birnin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Peter Obi ya barranta da Kwankwaso, ya fadi masu daukar nauyinta

Matasa da sauran yan kasa da su ka ce yunwa da talauci na yi masu illa sun shirya zanga-zanga ta kwanaki goma farawa daga 1 Agusta, 2024..

Nyesom Wike
Minista Nyesom Wike na tattaunawa da matasa domin hana zanga-zanga a Abuja Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a zantawarsa wasu matasa daga yankin Abuja ta Kudu domin hana zanga-zanga. Za a yi makamacin zaman da matasan Bwari da Gwagwalada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya gana da matasa kan zanga-zanga

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fadi dalilin ganawa da matasa domin ganin an hana gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya.

Ya ce su na wayar da kan matasan ne domin su fahimci illar da zanga-zanga za ta iya haifarwa Najeriya, Daily Post ta wallafa hakan.

"Bai kamata ayi zanga-zanga ba," Wike

Nyesom Wike ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta dade da cika shekara guda a kan mulki ba, saboda haka lokacin ya yi kadan a gane aikin da ta yi.

Kara karanta wannan

"Rashin cin zabe ne": Ministan Tinubu ya tona asirin wadanda ke shirya zanga zanga

Wike ya kara da cewa bai kamata a yi amfani da rigar zanga-zanga wajen tayar da hankulan jama'a ba.

Nyesom Wike wanda ya bayyana haka a kokarin dakile gudanar da zanga-zanga ya godewa sarakai duba da tsayin daka da su ka yi wajen wayar da kan al'ummarsu.

Zanga-zanga: Wike ya zargi 'yan siyasa

A baya mun kawo labari Minista Nyesom Wike ya yi zargin 'yan siyasar da su ka fadi zaben 2023 da kitsa manakisar gudanar da zanga-zanga a Najeriya saboda zafin kaye da su ka sha.

Nyesom Wike ya ba wa 'yan Najeriya hakuri, inda ya bayar da tabbacin cewa shugaba Bola Tinubu ya na iya bakin kokarinsa wajen daidaita lamura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.