Eagle Square: Shirin Zanga Zanga Ya Dauki Ɗumi, Matasa Sun Yi Wa Wike Zazzafan Martani

Eagle Square: Shirin Zanga Zanga Ya Dauki Ɗumi, Matasa Sun Yi Wa Wike Zazzafan Martani

  • Shugabannin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da matsi a Najeriya sun yi martani mai zafi ga ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Damilare Adenola ya bayyana matakin da za su dauka idan Nyesom Wike bai ba su damar amfani da dandalin Eagle Square ba
  • Matasan sun ce sun isar da takardar neman izinin amfani da dandalin amma ministan ya ce bai samu wata takarda kan haka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Magana kan zanga zanga na cigaba da daukan zafi yayin da kwanakin farawa ke kara matsowa kusa.

Kungiyar Take it Back Movement ta yi martani ga ministan Abuja, Nyesom Wike kan amfani da dandalin Eagle Square.

Kara karanta wannan

Kano: Ana so a raba shi da Kwankwaso, Gwamna Abba ya amince da ayyukan N36bn

Zanga zanga
Matasa sun dauki zafi kan maganar ministan Abuja wajen amfani da Eagle Square. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Daily Trust ta wallafa cewa daya daga cikin jagororin kungiyar, Damilare Adenola ne ya yi martanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga zanga a Eagle Square

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga masu son yin zanga zanga a dandalin Eagle Square su rubuta masa takardar neman izini.

Nyesom Wike ya kara da cewa za su biya kudin haya da cika sauran sharudda kafin a amince musu da amfani da dandalin.

'Yan zanga-zanga sun yi martani ga Wike

Daraktan kungiyar Take it Back Movement, Damilare Adenola ya ce sun riga sun mika takarda ga ofishin ministan tun ranar 26 ga watan Yuli.

Adenola ya ce babu yadda za a yi wanda talauci ya masa katutu yana neman mafita ta hanyar zanga zanga a ce sai ya biya kudin haya.

Matasa: 'Eagle Square na al'umma ne'

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

Daily Post ta wallafa cewa matashin ya ce dandalin Eagle Square na al'umma ne saboda haka ko Wike ya yarda, ko bai yarda ba za su yi zanga zanga.

Haka zalika, Daraktan Yiaga, Samson Itodo ya ce ya kamata gwamnati ta rika yi wa matasa bayani da zai kama hankali a kan zanga zangar.

Lauya ya yi magana kan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa hukumomi da malaman addini sun nuna fargaba kan cewa zanga zanga za ta iya haifar da tarzoma a fadin ƙasar nan.

Lauya mai fashin baki, Dr. Audu Bulama Bukarti ya bayyana hanyoyi biyar da za a bi wajen samun nasara a zanga zangar da kucewa tarzoma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng