Rai Bakon Duniya: Tsohon Kwamishina a Kaduna Ya Kwanta Dama
- An shiga jimami a jihar Kaduna bayan rasuwar tsohon kwamishina kuma fitaccen dan jarida a jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024
- Marigayin mai suna Alhaji Lawal Yusufu Saulawa ya rasu yana da shekaru 80 a duniya inda aka yi jana'izarsa a yau Lahadi a Kaduna
- Kafin rasuwar marigayin ya rike kwamishinan yada labarai a jihar Kaduna shekaru 40 da suka wuce da kuma aiki da BBC Hausa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Fitaccen dan jarida a Najeriya, Alhaji Lawal Yusufu Saulawa ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna.
Marigayin wanda tsohon kwamishina ne a jihar ya rasu a daren jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024 yana da shekaru 80.
Yaushe Saulawa ya rasu a Kaduna?
BBC Hausa ta tattaro cewa marigayin ya rasu a gidansa da ke Badikko a karamar hukumar Kaduna ta Kudu inda aka binne shi a makabartar Bashama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da sallar jana'izarsar masallacin Juma'a na Danfodio da ranar yau Lahadi 28 ga watan Yulin 2024.
Sallar jana'zarsa ta samu halartar manya mutane wadanda suka nuna alhini game da rasuwar marigayin.
Kaduna: Mukaman da Saulawa ya rike
Saulawa ya yi aiki da gidan jaridar BBC Hausa shekaru fiye da 40 da suka wuce kafin ya rike kwamishinan yada labarai a Kaduna.
Har ila yau, marigayin shi ne kwamishinan farko na yada labarai a jihar Katsina da sauran mukamai da dama.
Marigayin ya rasu ya bar mata uku da 'ya'ya guda 13 da kuma tulin jikoki da sauran 'yan uwa a bayansa.
Sanatan APC, Ubah ya rasu a Landan
A wani labarin, mun kawo muku labarin cewa an tafka babban rashin sanatan APC, Sanata Ifeanyi Ubah daga jihar Anambra.
Marigayin da ya wakilci Anambra ta Kudu ya rasu ne a birnin Landan da ke Burtaniya bayan ya sha fama da jinya na kankanin lokaci.
Majalisar Dattawa ta tabbatar mutuwar Ubah a jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024 inda ta ce an tafka babban rashin mutum nagari.
Asali: Legit.ng