“Na Gama Aiki Bani da Ko Kobo”: Tsohon Janar Din Soja Ya Ce Najeriya Bata Tsinana Masa Komai Ba
- Wani dattijon tsohon soja a Najeriya ya bayyana dana-sanin kasancewarsa dan Najeriya, ya bayyana halin da yake ciki
- A cewarsa, ya so a kasar Nambia aka haife shi ba a Najeriya ba, domin babu tsari da shiri a kasar nan ko kadan
- Tsoffin sojoji da sauran ma’aikatan gwamnati a Najeriya basu cika samun wani wadataccen kula ba, hakan na lalata rayuwarsu
FCT, Abuja - Wani tsohon janar din soja a Najeriya, Ishola Williams ya ce ya so ace shi dan wata kasa ce ba Najeriya ba.
Janar Williams dai ya shiga aikin soja a 1964, inda ya fara daga karamin jami’i har ya girma a aikin, kana ya yi ritaya a 1993.
Na bar aikin soja babu wani shiri
A wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Trust Tv, ya ce ya so ace a kasa kamar Namibia aka haife shi ba Najeriya ba, saboda kasa ce karama amma mai tsari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tuna rayuwarsa ta baya, ya ce ya bar aikin soja ba tare da wani shiri ko tsari ba, kana babu ko anini a asusunsa na banki.
A cewarsa, a baya ya nemi kafa kungiya mai zaman kanta, amma haka ya rasa damar saboda ba shi da ajiyayyun kudade duk da yiwa kasa bauta na tsawon lokaci.
Da kame-kame soja ya rayu sama da shekaru 30
Ya ce:
“Ina tsammanin na bar aiki a ranar 20 ga Nuwamba ko makamancin haka, 1993 kuma daga nan dole na yanke shawarar abin da zan yi da rayuwata. Na tafi ba tare da wani shiri ko tsari ba, ko da asusu na banki babu komai.
“Wasu mutane sun yi kokarin su taimake ni. Wani ya ba ni mota amma akwai matsaloli da yawa tare da ita, don haka sai na ajiye ta na fara hawa kabu-kabu.
Daga nan ya bayyana irin kame-kamen ayyuka da ya fara, har ta kai ga ya yi aiki da wata kungiya mai zaman kanta.
An tsinci gawar soja a daki
A wani labarin, an tsinci gawa wani sojan Najeriya da ya yi ritaya, mai suna Kanal BT Vandi, a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.
An tsinci gawar marigayin ne a sansanin ‘Defence Academy’ da ke kan titin Vom, a birnin Jos.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa sojan mai ritaya ya rasu ne a dakinsa bayan ya shiga ciki da wasu 'yan sa'o'i kadan.
Asali: Legit.ng