Rundunar 'yan Sanda ta Gano Manyan Matsalolin da Zanga Zanga Za Ta Iya Haifarwa
- Hadakar hukumomin tsaro sun kammala daukar matakai a kan masu niyyar fita zanga-zanga ranar 1 Agusta, 2024
- A wata hira da ta kebanta da Legit, rundunar 'yan sandan Jigawa ta bayyana cewa ta zauna da masu ruwa da tsaki a kokarin shawo kan jama'a
- Jami'an hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam ya ce sun gudanar da gagarumin taro domin dakile zanga zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa - Yayin da ya rage kwanaki uku a fara zanga-zangar gama gari a kasar nan, rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta fitar da tsare-tsaren tunkarar lamarin.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana cewa sun yi kokarin nusar da jama'a illar gudanar da zanga-zanga.
DSP Lawan Shiisu Adam ya shaidawa Legit cewa sun zauna da masu ruwa da tsaki, daga ciki har da sarakuna, malaman addini, hukumomi, kungiyoyi masu zaman kansu da mata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fargabar 'yan sanda a kan zanga-zanga
Rundunar 'yan sanda ta bayyana tsoron tsunduma tashe-tashen hankula da wargajewar al'umma a lokacin zanga-zanga.
DSP Lawan Shiisu Adam da ke magana da yawun rundunar reshen jihar Jigawa ne ya bayyana haka, inda ya bayyana wasu daga matsalolin da za a iya samu;
1. Miyagu za su shiga zanga-zanga
DSP Adam ya ce akwai fargabar wadanda za su tayar da tarzoma tuni su ka kammala shirin jawo tashe-tashen hankula ta rigar masu zanga-zanga.
Ya ce akwai wasu kasashen ketare da za a iya ganin yadda miyagu su ka shiga cikin masu zanga-zanga. kuma har yanzu ana fama da matsalolin tsaro.
2. Lalata dukiyoyin jama'a a lokacin zanga-zanga
Kakakin rundunar 'yan sandan Jigawa ya shaida cewa akwai fargabar wasu bata gari ka iya amfani da rigar zanga-zanga wurin lalata kayan jama'a.
DSP Lawan Shiisu Adam ya kara da cewa idan aka samu irin wannan akasi, za a iya lalata kadarorin gwamnati, dukiyoyin jama'a, rumbunan abinci da satar kayan 'yan kasuwa.
3. Asarar rayukan idan miyagu sun shiga zanga-zanga
'Yan sanda Jigawa sun bayyana cewa akwai fargabar idan zanga-zanga ta sauya launi daga kalar lumana zuwa tashin hankali za a samu asarar rayuka.
Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam ya ce barin zanga-zanga da hawa teburin tattaunawa shi zai fi alheri.
Zanga-zanga: Yan sanda za su bayar da tsaro
A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana shirinta na dakile tashe-tashen hankula yayin zanga-zangar kwanaki 10 da 'yan kasa ke shirin yi.
Rundunar reshen babban birnin tarayya Abuja ta ce za ta tura jami'anta 4,200 zuwa lungu da sakon birnin a kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin jama'a yayin zanga-zanga.
Asali: Legit.ng