Ana Harin Zanga Zanga, Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Muhimmin Mataki

Ana Harin Zanga Zanga, Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Muhimmin Mataki

  • Gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin ƙasar nan yayin da ake shirin fara zanga-zanga
  • Hukumar kula da shige da fice da ƙasa ta umarci jami'anta da su sanya ido sosai a lokacin gudanar da zanga-zangar
  • An tsaurara matakan tsaron ne domin hana ƴan ƙasashen waje shigowa cikin ƙasar nan domin tada zaune tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin ƙasar nan yayin da ake shirin fara zanga-zanga.

Zanga-zangar dai an shirya fara gudanar da ita ne a ranar, 1 ga watan Agusta domin nuna adawa da halin ƙuncin da a ke ciki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

Gwamnatin tarayya ta tsaurara matakan tsaro
Gwamnatin tarayya ta tsaurara tsaro a iyakokin kasar nan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Hukumar NIS ta tsaurara tsaro

Kwanturola janar ta hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), Kemi Nandap, ta bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar, Kenneth Udo, ya fitar ranar Asabar a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kemi Nandap ta umurci dukkanin shugabannin hukumar na shiyya-shiyya da na jihohi da su yi taka tsan-tsan.

Ta ce ya kamata jami’an hukumar su ƙara sanya ido kan zanga-zangar wacce wasu ƙungiyoyi ke shirin yi a faɗin ƙasar nan, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Meyasa aka tsaurara tsaron?

Kemi Nandap ta ce wannan umarnin an ba da shi ne domin tabbatar da cewa wasu ƴan ƙasashen waje ba su shigo cikin ƙasar nan domin shiga cikin zanga-zangar ba.

"Dangane da alhakin kare iyakokin ƙasar nan da aka ɗora a wuyan hukumar, an ɗorawa jami’ai musamman shugabanni alhakin tashi tsaye domin tabbatar da hakan."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi watsi da batun zanga zanga, ya fadi matakan da ya dauka

"Wannan shi ne ta hanyar tabbatar da cewa babu wani ɗan ƙasar waje da zai iya yin amfani da zanga-zangar domin tada zaune tsaye a ƙasar nan."

- Kenneth Udo

Hukumar ta ba da umarnin dakatar da dukkanin hutu na wucin gadi na jami'anta tare da yin kira ga jami’an da su nuna matuƙar ƙwarewa da kishin ƙasa wajen gudanar da ayyukansu.

Ksranta wasu labaran kan zanga-zanga

Ƙungiyar ZIEM ta fice daga zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan asalin jihar Zamfara (ZIEF) ta sanar da janyewa daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanin haƙiƙanin shugabannin da za su jagoranci zanga-zangar a ƙasa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng