Tinubu Ya Yi Jawabi Inda Ya Dawo da Tallafin Mai, Wutar Lantarki? Gaskiya Ta Fito
- Gwamnatin Tarayya a karyata wata sanarwa da ke yawo cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi kan matsin tattalin arziki
- A cikin jawabin da ake yadawa, an ce shugaban ya dawo da tallafin mai da na wutar lantarki da rage yawan Ministoci
- Sai kuma rushe ofishin matar shugaban kasa da hana jami'an gwamnati fita kasashen ketare da sauran matakai domin rage radadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan wata sanarwa da ke yawo a kafofin sadarwa cewa Bola Tinubu ya yi jawabi.
Gwamnatin ta ce babu inda Tinubu ya yi jawabi ciki har da dawo da tallafin mai da na wutar lantarki domin dakile zanga-zanga.
Halin kunci: Gwamnatin Tinubu ta yi magana
Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga shi ya fadi haka a shafinsa na X a daren jiya Asabar 27 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya ce babu gaskiya a jawabin kuma wasu bata-gari ne suka hada domin kawo tsaiko a cikin al'ummar Najeriya.
Ya ce babu inda Tinubu ya yi jawabi kan matsin tattalin arziki da yake cewa zai rage albashin mukarraban gwamnati da 50%.
Alkawuran da Tinubu ya yi a jawabin
Sauran alkawuran a cikin jawabin da ake yadawa sune rushe ofishin matar shugaban kasa da rage yawan Ministoci.
Sai kuma siyar da jiragen shugaban kasa da ba su da amfani da kuma hana jami'an gwamnatin fita ketare neman lafiya.
An yi ta yada jita-jitar cewa Tinubu ya yi jawabi musamman ganin yadda ake shirin fita zanga-zanga inda yake ba matasa hakuri.
A cikin jawabin da ake yadawa, Tinubu ya ce ya san halin da ake ciki amma ya roki matasa su sake ba shi dama domin aiwatar da tsare-tsaren da ya kawo.
'Yan sanda sun gidaya sharuda kan zanga-zanga
Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a Najeriya ta amince da yi zanga-zanga amma ta lumana tare da gindaya wasu sharuda.
Rundunar ta ce za ta ba da kariya amma matasan za su tura bayanansu ga kwamishinonin jihohinsu domin samar da tsaro.
Asali: Legit.ng