Ku Kara Hakuri: Ministan Tinubu Ya Ba ’Yan Arewa Shawari Kan Zanga-Zangar da Ake Shirin Yi
- Ministan Tinubu ya ce 'yan zanga-zanga na son kawo sharri ga Najeriya a madadin dago batun gyara
- Ya ce Tinubu na kokarin a gyara kasar nan ta fannoni da dama, ciki har da tattalin arziki, tsaro da samar da abinci
- A fahimtar minista, shekara da 'yan kwanaki sun yi kadan wajen yiwa gwamnatin Tinubu hukuncin kisa
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Sokoto - Karamin ministan albarkatun ruwa a gwamnatin Tinubu, Bello Goronyo ya ce ya yi wuri 'yan Najeriya su fara kukan yunwa a mulkin Tinubu.
A nasa fahimtar, shekaru guda ta yi kadan wajen yankewa gwamnatin Tinubu hukuncin alkiblar da aka dosa kai tsaye, Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gwamnatin jihar Sokoto ta shirya kan batun da ya shafi shiryayyen zanga-zangar da aka tsara a ranar 1 ga watan Yuli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zanga na son bata kasa
Da yake jawabi a ranar Juma'a, ministan ya ce:
"Wadannan mutanen a kage suke su durkusar da kasa. Manufarsu ba shugaban kasa bane. Suna nufin wargaza kasa ne. Suna son tarwatsa mu ne kamar yadda aka tarwatsa kasashe irin Sudan.
"Shugaban kasa ya fadi tun farkon hawansa cewa, za a kawo sauye-sauyen da ba a yi tsammani ba. Ya gaji arziki da akasin haka daga maganinsa kuma ya saduda. Don haka, shekara guda da watanni biyu sun yi kadan wajen yiwa gwamnatinsa hukunci."
Ayyukan da Tinubu ya maida hankali gare su
Goroya ya kara da cewa, gwamnatin Tinubu na yin mai yiwuwa daidai gwargwado don tabbatar da an yaki yunwa, fatara da rashin tsaro a Najeriya.
Ya ce:
"Ana ta kokarin wajen ganin an kawo karshen rashin tsaro wanda ba za mu iya bayyanawa a fili ba saboda sablon yaki, amma wadanda suka sani sun sani."
Ya kuma kara da cewa, a karon farko gwamnati ta bude madatsan ruwa domin noman rani, inda yace akwai madatsan ruwa 408 da za a yi amfani da su nan gaba.
Daga karshe ya yabawa gwamnati wajen kafa hukumar ci gaban Arewa maso Yamma da kuma ma'aikatar dabbobi.
Talauci ke damun 'yan zanga-zanga, inji mawaki
A wani labarin, fitaccen mawaki a Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya yi magana kan masu zanga-zanga.
Portable ya ce ba zai taba fita zanga-zanga ba da ake shirin yi musamman saboda halin kunci da ake fama da shi a kasar.
Mawakin ya fadi haka a wani faifan bidiyon Instagram inda ya ce a shekarar 2020 an dama da shi a wurin zanga-zanga amma yanzu ya samu cigaba.
Asali: Legit.ng