Zanga Zanga: Fitaccen Basarake Ya Tsoma Baki, Ya Roki ’Yan Najeriya Abu 1

Zanga Zanga: Fitaccen Basarake Ya Tsoma Baki, Ya Roki ’Yan Najeriya Abu 1

  • Fitaccen basarake a jihar Ondo, Oba Aladetoyinbo Ogunlade ya yi magana kan shirin zanga-zanga da matasa ke yi
  • Basaraken ya roki 'yan Najeriya da su sake ba Bola Tinubu lokaci inda ya ce za su ji dadi nan ba da jimawa ba a fadin kasar
  • Wannan rokon na zuwa ne yayin da matasa a Najeriya ke shirin fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Fitaccen basarake a jihar Ondo ya roki 'yan Najeriya kan shirinsu na fita zanga-zanga game da halin kunci.

Deji na Akure, Oba Dakta Aladetoyinbo Ogunlade ya bukaci 'yan kasar su sake ba Bola Tinubu lokaci domin shawo kan matsalolin.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa zanga-zangar cire tallafi a mulkin Jonathan ba a samu rigima ba'

Basarake ya roki 'yan Najeriya ba Tinubu dama madadin zanga-zanga
Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Ogunlade ya roki 'yan Najeriya alfarma madadin zanga-zanga. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, DEJI of AKURE Kingdom.
Asali: Facebook

Zanga-zanga: Basarake ya roki ba Tinubu lokaci

Basaraken ya fadi haka ne a yau Asabar 27 ga watan Yulin 2024 bayan wata ganawa ta musamman a birnin Abeokuta, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oba Ogunlade ya ce'yan Najeriya za su yi murna har su bukaci Tinubu ya kara wa'adi na biyu idan suka ba shi lokaci.

Ya ce mutane su rika duba misalin jihar Lagos yadda Tinubu ya same ta da kuma yadda ya sauya tattalin arzikinta, Punch ta tattaro.

Basarake ya fadi kokarin Tinubu a Lagos

"Wannan shekara daya kawai ya yi, ya kamata a kara masa lokaci har zuwa lokacin da zai kammala wa'adin farko."
"Kun sani lokacin da ya karbi jihar Lagos tattalin arzikinta a lalace ya ke amma ya ba da mamaki, ya kamata a sake ba shi dama."

Kara karanta wannan

Mai neman takaran shugaban kasa ya dora alhakin zanga zanga a kan Bola Tinubu

- Aladetoyinbo Ogunlade

'Yan sanda sun gidaya sharuda kan zanga-zanga

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a Najeriya ta amince da yi zanga-zanga amma ta lumana tare da gindaya wasu sharuda.

Rundunar ta ce za ta ba da kariya amma matasan za su tura bayanansu ga kwamishinonin jihohinsu domin samar da tsaro.

Wannan na zuwa ne yayin da matasa a Najeriya ke shirin fita zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agustan 2024 da muke ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.