An Kai ’Yan Arewa Bango: Matasa sun Dauki Matakin Kawo Karshen Asusun Rarara a Facebook

An Kai ’Yan Arewa Bango: Matasa sun Dauki Matakin Kawo Karshen Asusun Rarara a Facebook

  • Matasan Arewa sun kawo karshen shafin Rarara a manhajar Facebook bayan ya saki wakar yabon gwamnatin Tinubu
  • An sace mahaifiyar Rarara a kwanakin baya, lamarin da ya jawo musayar ra'ayi a kafafen sada zumunta musamman a Arewa
  • 'Yan Arewa na yiwa Rarara kallon wanda bai yiwa 'yan yankin adalci ba, inda suka kai kararsa kamfanin Meta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Arewacin Najeriya - Alamu masu karfi na nuna cewa, matasan Arewacin Najeriya sun gaji da wulakanci da raini daga mawakan siyasa da 'yan koronsu.

A yau Asabar 27 ga watan Yuli aka nemi asusun mawakin jam'iyyar, Dauda Kahutu Rarara aka rasa a kafar sada zumunta ta Facebook.

Kara karanta wannan

Haba Kahutu Rarara: Jama'a sun shiga rudani bayan Rarara ya saki sabuwar wakar yabon Tinubu

Wannan na zuwa ne bayan da ya wake shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da yaba masa kan abubuwan da ke faruwa a kasar nan.

An goge asusun Rarara a kafar Facebook
An sauke asusun Rarara na Facebook | Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakar Rarara ta kai ga matasa sun dauki mataki

Tun bayan da ya saki wakar 'yan Arewa ke masa kallon wanda bai yiwa 'yan adalci ba, musamman duba da yadda a baya aka sace mahaifiyarsa.

Rarara dai na daga mawakan Arewa da ke zalakar harshe mai kaifi wajen yaba 'yan siyasa da ayyukan da suke yi.

A wannan karon, 'yan Arewa na ganin Rarara ya cika zakewa wajen babatu kan gwamnatin Tinubu da ta gaza samar da zaman lafiya a Arewa, wanda shi kansa Rarara shaida ne.

Ina asusun Facebook na Rarara ya yi?

Duban da Legit Hausa ta yi, an rasa asusun ne da yammacin Asabar bayan da matasa suka dukufa wajen kai rahoton rashin amincewa da zubin wakar da ba shafin na Rarara.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Matasan sun ci gaba da yada bukatar duk wani dan Arewa ya kokarta kai rahoton mawaki ga duk kamfanonin shafukan sada zumunta, ciki har da TikTok.

A halin yanzu, 'yan Arewa a fusace suke, inda suka dage da fara zanga-zangar lumana a ranar 1 ga watan Agusta don nuna kin jinin dokoki masu tsauri na gwamnatin Tinubu.

'Yan Najeriya sun yiwa Rarara wankin babban bargo

A baya kun ji cewa, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da tunzura da lamarin gwamnatin kasar; musamman 'yan Arewa, fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya saki sabuwar wakar yabon gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan da 'yan bindiga suka saki mahaifiyar Rarara da suka sace na tsawon kwanaki sama da 20.

A sabon bidiyon da Rarara ya saki, an ji yana yabawa Tinubu ta fannin tsaro, wadatar abinci da sauran ababen more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.