NYSC Ta Fadi Tsarinta Kan Masu Bautar Kasa Game da Zanga Zanga, Ta Jero Dalilai

NYSC Ta Fadi Tsarinta Kan Masu Bautar Kasa Game da Zanga Zanga, Ta Jero Dalilai

  • Hukumar kula da matsasa masu yiwa kasa hidima ta NYSC ta yi gargadi kan shiga zanga-zanga musamman masu bautar kasa
  • Hukumar ta ce shiga zanga-zanga a zahiri ko ta yanar gizo ya saba tsarin hukumar wurin tabbatar da zaman lafiya
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani matashi mai bautar ƙasa kan wannan doka ta hukumar NYSC game da shirin zanga-zanga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar matasa masu yiwa kasa hidima ta (NYSC) ta yi magana kan shirin zanga-zanga a Najeriya.

Hukumar ta gargadi matasa da ke yiwa kasa hidima da su guji zurma kansu a lamarin zanga-zangar da za a yi a makon gobe.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga: Peter Obi ya barranta da Kwankwaso, ya fadi masu daukar nauyinta

Hukumar NYSC ta gargadi matasa masu bautar kasa kan zanga-zanga
Hukumar NYSC ta haramta zanga-zanga ga matasa masu bautar kasa. Hoto: @officialnyscng.
Asali: Twitter

Zanga-zanga: NYSC ta yi magana ga matasa

Kwadinetan hukumar a jihar Lagos, Yetunde Baderinwa shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baderinwa ya ce kamata ya yi masu bautar kasa su tabbatar da hadin kan kasa a duk inda suke ba tare da kawo rarrabuwa ba.

Ya ce NYSC ta na da tsare-tsare da dokoki da suka haramtawa matasa masu bautar kasa shiga lamarin zanga-zanga, Sahara Reporters ta tattaro.

NYSC ta yi gargadi game da zanga-zanga

"Dole ne kowane matashi mai bautar kasa ya bi dokokin da aka gindaya masa, na tsare-tsaren hukumar NYSC na hadin kai a kasa, ya kamata mu tunatar da masu bautar kasa su tabbatar da bin dokokinmu."
"Ya sabawa dokar hukumar NYSC wani daga cikinmu ya shiga zanga-zanga a zahiri ko kuma ta yanar gizo."

Kara karanta wannan

"Ba Lagos a ciki": Diyar Tinubu ta yi magana kan zanga zanga, ta shawarci iyaye

"Shiga zanga-zanga ya saba musabbabin kafa hukumar da tsare-tsarenta wurin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya."

- Yetunde Baderinwa

Baderinwa ya ce duk wani matashi da aka kama da saba dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani daga hukumar NYSC.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani matashi mai bautar ƙasa kan wannan doka ta hukumar NYSC.

Yusuf Muhammad da ke bautar ƙasa a jihar Borno ya ce ai daman ba da kayan NYSC za su fita ba idan suna so.

"Idan har ina son fita ai da kayan gida zan je kuma babu wanda zai san ni 'Corper' ne."
"Muna fatan a yi lafiya kuma a karkare lafiya amma dai dokarsu za ta yi aiki ne kan wanda ke da kayan NYSC a jikinsa."

- Yusuf Muhammad

'Yan sanda sun gidaya sharuda kan zanga-zanga

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda a Najeriya ta amince da yin zanga-zanga amma ta lumana tare da gindaya wasu sharuda.

Rundunar ta ce za ta ba da kariya amma matasan za su tura bayanansu ga kwamishinonin jihohinsu domin samar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.