Haba Kahutu Rarara: Jama’a Sun Shiga Rudani Bayan Rarara ya Saki Sabuwar Wakar Yabon Tinubu

Haba Kahutu Rarara: Jama’a Sun Shiga Rudani Bayan Rarara ya Saki Sabuwar Wakar Yabon Tinubu

  • 'Yan Najeriya da dama na mamakin yadda Rarara ya sake yiwa Tinubu waka kan yadda halin kasar nan ke ciki
  • A madadin ya yi wakar nuna damuwa da halin da kasar nan ke ciki na matsi, Rarara ya saki sabuwar wakar da ke yaba abin da Tinubu ke yi
  • An sace mahaifiyar Rarara kwanakin baya, wanda hakan ya dauki hankalin 'yan Arewacin Najeriya da dama

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da tunzura da lamarin gwamnatin kasar; musamman 'yan Arewa, fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya saki sabuwar wakar yabon gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Kara karanta wannan

An kai 'yan Arewa bango: Matasa sun dauki matakin kawo karshen asusun Rarara a Facebook

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan da 'yan bindiga suka saki mahaifiyar Rarara da suka sace na tsawon kwanaki sama da 20.

'Yan Najeriya sun fusata da wakar Rarara
'Yan Najeriya sun yiwa Rarara dirar mikiya a kafar sada zumunta | Hoto: Dauda Kahutu Rarara, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A sabon bidiyon da Rarara ya saki, an ji yana yabawa Tinubu ta fannin tsaro, wadatar abinci da sauran ababen more rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda a baya aka sace mahaifiyar Rarara

A baya idan baku manta ba, 'yan Najeriya da yawa sun taya Rarara jimami yayin da 'yan bindiga suka shigo har gida suka sace mahaifiyarsa.

Wasu kuwa, suna tofin Allah shi kara bisa ga yadda mawakin ke azarbabi wajen yaba gwamnatin da wasu ke ganin ta daure marar 'yan kasa.

Sai dai, kwanaki kadan da nasarar da aka samu har mahaifiyarsa ta dawo, Rarara ya yiwa Tinubu wakar yabo bisa yaye kananan hukumomi daga nonon gwamnatin jihohi.

'Yan Najeriya sun yi mamakin sabuwar wakar Rarara

Kara karanta wannan

Mai neman takaran shugaban kasa ya dora alhakin zanga zanga a kan Bola Tinubu

A bangare guda, 'yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta sun nuna damuwa da yiwa Rarara kallon kola bisa sake bin ta gwamnatin Tinubu.

Da yawansu sukan dasa ayar tambayar cewa, ta yaya mawakin zai yaba gwamnatin APC a fannin tsaro duba da yadda mahaifiyarsa ta sha tsami a daji a hannun tsagerun 'yan bindiga.

Wasu kuwa, na yiwa kallon sace mahaifiyar Rarara kallon wata manakisa da aka shirya a siyasance don dauke hankalin 'yan Najeriya kan wasu lamurra.

Yadda aka sako mahaifiyar Rarara

A baya kadan, rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa 'yan bindiga sun sako mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara bayan shafe akalla mako 2 a tsare.

A ranar Juma'a, 28 ga watan Yunin 2024 muka ruwaito cewa 'yan bindiga sun kutsa sabon gidan Rarara da ke gabashin Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja inda suka sace mahaifiyarsa.

Fitaccen mawakin, Rarara ne ya sanar da kubutar mahaifiyarsa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a safiyar ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.