Fargabar Zanga Zanga: Tinubu Ya Dawo Biyan Al’umma Tallafi, an Ci Moriyar Arzikin Kasa

Fargabar Zanga Zanga: Tinubu Ya Dawo Biyan Al’umma Tallafi, an Ci Moriyar Arzikin Kasa

  • Gwamnatin Tarayya ta dawo da tsarin ba da tallafi ga gidaje na Conditional Cash Transfer (CCT) yayin da ake shirin zanga-zanga
  • Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da tsarin ne a kwanakin baya bayan zargin almundahana game da shirye-shiryen
  • Hakan bai rasa nasaba da barazanar zanga-zanga da ake yi musamman saboda halin kunci da aka jefa jama'a a ciki a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun ya tabbatar da cigaba da biyan tallafi na CCT na Gwamnatin Tarayya.

Edun ya ce a yanzu akalla gidaje 600,000 ne suka ci gajiyar tallafin bayan dawowa cigaba da biyan kudaden.

Tinubu ya dawo da rabon tallafi ga 'yan kasa yayin da ake shirin zanga-zanga
Akalla gidaje 600,000 suka ci gajiyar tallafin CCT bayan Tinubu ya dawo da shi. Hoto: @officialABAT.
Asali: Twitter

Gidajen da suka ci gajiyar tallafin Tinubu

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa zanga-zangar cire tallafi a mulkin Jonathan ba a samu rigima ba'

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani babban taro kan ayyukan Ministoci a kasar, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta himmatu wurin habaka tattalin arzikin kasar domin samun cigaba da rage radadin da ake ciki.

"Bayan dawo da ba da tallafin, akalla gidaje 600,000 ne suka ci gajiyar talafin kudin a wannan mako da muke ciki."

- Wale Edun

Har ila yau, Edun ya ce tabbas ana cikin wani hali amma na wani lokaci ne inda ya ce nan ba da jimawa ba za a caba, TheCable ta tattaro.

Ya ce tsare-tsaren gwamnatin sun fara haifar da 'da mai ido idan aka kwatanta da farashin kaya na shekarar da ta gabata.

Musabbabin dakatar da shirin CCT na Tinubu

Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya umarci sake duba kan tsarin CCT wanda ke karkashin hukumar jin kai ta NSIPA.

Kara karanta wannan

"Tattalin arzikin 2023 ya ɗara na 2023 da kaso mai tsoka" Inji Gwamnatin Tinubu

Daga bisani shugaban ya dakatar da shirye-shiryen karkashin NSIPA bayan zargin almundahana daga ma'aikatar.

Ganduje ya gana da ciyamomi a jihohi

Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kira wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a da ke fadin kasar.

Ganawar ba ta rasa nasaba da shirin zanga-zanga a fadin kasar da matasa suka shirya saboda mawuyacin hali da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.