‘Abin da Ya Sa Zanga Zangar Cire Tallafi a Mulkin Jonathan Ba a Samu Rigima Ba’
- Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, tsohon daraktan hukumar DSS ya yi magana kan abubuwan da suka faru a baya
- Ejiofor ya akwai bambanci a lokacin zanga-zangar cire tallafi a 2012 da yanzu ganin yadda abubuwa suka bambanta
- Ya ce a yanzu mutane a fusace suke saboda halin kunci da tsadar rayuwa sabanin wancan lokaci duba da yadda shugaban yake
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon daraktan hukumar DSS, Mike Ejiofor ya yi magana kan zanga-zanga a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Tsohon daraktan ya ce ba a samu hatsaniya a lokacin zanga-zangar cire tallafi na 2012 saboda yadda tsarinsa ya ke.
Zanga-zanga: Bambanci a lokacin Jonathan da yanzu
Ejiofor ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Arise a jiya Juma'a 26 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon daraktan hukumar DSS ya ce daga cikin dalilan da ba a samu matsala ba shi ne lokacin tsadar rayuwa ba ta kai yadda ake ciki yanzu ba.
Ya ce yanzu mutane suna cikin yunwa da tsadar rayuwa wanda ya tilasta su neman duk wata hanya domin sauke fushinsu, cewar Vanguard.
"Zanga-zangar 2012 ba ta koma rigima ba saboda yadda shugaban yake wurin ba da damar ayi komai cikin lumana."
"Wahalar da ake ciki a wancan lokacin ba ta kai kwatankwacin na yanzu ba saboda yanzu mutane a fusace su ke suna neman inda za su sauke fushinsu."
"Yana daga cikin 'yancinsu yin zanga-zanga amma da ya kamata su ba gwamnatin bayanai kan shirinsu ganin yadda ake rokon su janye kudirinsu."
- Mike Ejiofor
'Yan sanda sun gindaya sharuda kan zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta ba da damar yin zanga-zanga amma ta kasance cikin lumana ba tashin hankali.
Daga cikin sharudan shi ne shugabannin zanga-zangar su ba da bayanansu ga kwamishinonin 'yan sanda da ke jihohinsu daban-daban.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin fita zanga-zanga a fadin kasar saboda mawuyacin hali da ake ciki da kuma tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng