ATBU: Ɗalibar Jami'a Ta Rasu Bayan Shiga Wanka a Wani Yanayi Mai Ruɗani a Arewa
- Wata ɗalibar aji uku a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Naja'atu Salisu ta rasu bayan ta shiga wanka da safiyar Jumu'a
- Rahotanni sun bayyana cewa babu wanda ya san abin da ya faru bayan ta shiga banɗakin, sai dai aka ɗauko ta rai hannun Allah
- Mai magana da yawun jami'ar ATBU, Zailani Bappa ya ce an yi kokarin kai ta asibiti amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Ɗalibar aji uku a jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi (ATBU), Naja'atu Salisu ta riga mu gidan gaskiya tana tsakiyar wanka a banɗaki.
Ɗalibar wacce ke karatu a fannin ilimin na'ura mai kwakwalwa ta rasu ne bayan an ɗauko ta rai hannun Allah a banɗaki da safiyar ranar Jumu'a.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Naja'atu ta shiga banɗakin mata a gidan kwanan ɗalibai da ke Gubi da niyyar yin wanka domin shirya zuwa lakca.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai daga bisani aka ɗauko ta ko motsi ba ta yi daga banɗakin kuma daga bisani rai ya yi halinsa.
Ƴar ɗakinsu Naja'atu wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
"Ta gama duk wasu ayyuka da ta saba yi na shirye-shiryen tafiya karatu kafin ta shiga wanka. Ta ɗauko kalar tufafin da take son sa wa a ranar ta ajiye a gefen gadonta."
Jami'ar ATBU ta tabbatar da lamarin
Mai magana da yawun jami'ar ATBU, Zailani Bappa, ya tabbatar da lamarin da cewa an yi gaggawar kai ta asibitin cikin makaranta amma likitoci suka gaza kama jijiya a jikinta.
"Bayan an lura da haka ne aka garzaya da Naja’atu zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar ATBU inda likitoci suka tabbatar da ta rasu” inji shi.
Zailani Bappa ya ce an yi jana’izar Naja’atu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kana ya yi mata addu’ar Allah ya jikan ta.
IG ya yi zargin shigo da sojojin haya
Ku na da labarin Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bayyana cewa an shigo da sojojin haya daga ketare domin gurɓata zanga-zangar da ƴan Najeriya ke shirin yi.
IGP Kayode Egbetokun ya gargaɗi matasa su guji shiga duk wani gungu da suka ci karo da shi a lokacin wannan zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng