'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Sun Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Sun Kashe Bayin Allah

  • Yan bindiga sun kashe mutane biyar a cikin masallacin kauyen Katakpa da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa
  • Rahotanni daga mazauna kauyen sun nuna cewa waɗanda maharan suka kashe sun gudo ne daga garuruwansu saboda yawaitar hare-hare
  • Shugaban ƙaramar hukumar Toto, Alhaji Abdullahi Aliyu Tashas ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Ƴan bindiga sun kai kazamin farmaki kan bayin Allah a masallaci a kauyen Katakpa da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun hallaka mutane biyar a masallacin a lokacin harin gabanin ƙarisowar dakarun sojoji.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Yan bindiga sun kashe mutum biyar a masallaci a jihar Nasarawa Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya da tattaro cewa mutanen da maharan suka kashe ƴan gudun hijira ne da suka baro gudajensu saboda yawaitar hare-hare, suka koma zama a masallaci.

Kara karanta wannan

Kwara: Miyagun 'yan bindiga sun farmaki masu ibada, 'yan sanda sun kai daukin gaggawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin kauyen, Ibrahim Yakubu ya bayyana cewa maharan sun shigo garin da tsakar dare misalin karfe 2:00 na safiyar Alhamis, suka tafka wannan ta'asa a Masallacin.

Ya ƙara da cewa dakarun sojoji sun yi koƙarin kawo ɗauki kauyen bayan samun labarin harin, inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigar.

Sojoji sun kashe mahara da dama

Ibrahim ya ce bayan gumurzu da ƴan ta'addan, dakarun sojoji sun samu nasarar tura da yawa daga cikin maharan zuwa lahira.

A cewar mutumin, maharan sun ajiye baburansu a wajen gari, kana suka shigo kauyen a ƙafa cikin dare a lokacin da mutane suka yi nisa a barci.

Shugaban ƙaramar hukumar Toto a jhar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Aliyu Tashas, ya tabbatar da kai harin amma bai yi cikakken bayani ba.

Bayanai sun nuna cewa daga watan Fabrairu, 2024 zuwa yau, mahara sun kashe dagaci da dakarun sojoji da dama a kauyen Katapka a hare-hare daban-daban da suka kai.

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

Bam ya fashe a kasuwa a Yobe

A wani rahoton kuma wani abin fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya tashi a kasuwar shanu da ke garin Buni Yadi a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan tashin bam ɗin, sojoji sun sake gano wani bam da aka dasa a kasuwar amma sun kwance shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262