'Yan Sanda Sun Ba Matasa Damar Zanga Zanga, Sun Gindaya Musu Sharuda Masu Tsauri
- Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta ba matasa masu shirin zanga-zanga damar gudanar da ita cikin lumana ba tare da matsala ba
- Rundunar ta bukaci duka kungiyoyin da ke cikin zanga-zangar su ba da bayansu da na shugabanninsu a hukumance
- Sufeta Janar Kayode Egbetokun ya tura bukatar inda ya ce hakan zai ba su damar dakile bata-gari a cikin shirin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sanda a Najeriya ta tura sako mai muhimmanci ga matasa masu shirin zanga-zanga.
Rundunar ta bukaci duka masu shirya zanga-zangar su rubuta takarda zuwa ga kwamishinonin ƴan sanda a jihohinsu daban-daban.
Zanga-zanga: Ƴan sanda sun gindaya sharuɗa
Babban Sifetan ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Egbetokun ya ce sun dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gudanar da zanga-zangar cikin kwanciyar hankali, Channels TV ta tattaro.
Ya ce ya kamata duka kungiyoyin da ke cikin zanga-zangar su ba da bayanansu da shugabanninsu domin gudanarwa cikin lumana.
Sufeta Janar ya ce hakan ne zai ba su damar zakulo bata-gari da ke son kawo cikas a shirin zanga-zangar.
Ƴan sanda sun bukaci zanga-zangar lumana
"Mu na sane da ƴancin ƴan Najeriya na yin taro da kuma gudanar da zanga-zangar lumana."
"Saboda samun zaman lafiya, mu na kira ga masu zanga-zanga su mika bayanansu ga kwamishinonin ƴan sanda a jihohinsu inda za a gudanar da zanga-zanga."
"Ya kamata su fadi inda za su yi taron da dalilin zanga-zangar da lokacin da za ta dauka da kuma lambobin shugabancinsu."
- Kayode Egbetokun
Ƴan sanda sun jibge jami'ai a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya, rundunar 'yan sanda ta dauki mataki a birnin Abuja.
Rundunar ta baza jami'anta 4,200 lungu da sakon birnin domin dakile tashin hankali yayin zanga-zangar da za a yi.
Ƴan sandan suka ce sun dauki wannan mataki ne domin kare rayuwa da kuma dukiyoyin al'umma saboda zargin shigar miyagu ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng