Malaman Musulunci Sun Sake Magana Kan Zanga Zanga, Sun Fadi Manaƙisar da Ke Ciki

Malaman Musulunci Sun Sake Magana Kan Zanga Zanga, Sun Fadi Manaƙisar da Ke Ciki

  • Malaman Musulunci a jihar Ogun sun bayyana matsayarsu kan shirin zanga-zanga da matasa za su yi a fadin kasar baki daya
  • Jagororin addinin sun bayyana damuwa kan yadda wasu ke kokarin amfani da zanga-zangar wurin kawo rigima da tashin hankali
  • Hakan bai rasa nasaba da halin kunci da ake ciki wanda shi ne musabbabin shirya wannan zanga-zanga a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Gamayyar malaman Musulunci a jihar Ogun sun yi Allah wadai da shirin gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya.

Malaman Musulunci suka ce ba a bukatar zanga-zangar a wannan lokaci inda suka ce hakan zai kawo rigima ne da koma baya.

Kara karanta wannan

"A rungumi zaman lafiya": Malam Izala da Darika sun yi magana bayan ganawa da Tinubu

Malaman Musulunci sun yi martani kan masu shirin zanga-zanga
Malaman Musulunci a jihar Ogun sun gargadi masu zanga-zanga. Hoto: Legit.
Asali: Original

Malaman Musulunci sun gargadi masu shirin zanga-zanga

Limaman sun bayyana haka a wani taro da jami'an tsaro a babban masallacin Juma'a na Kobiti da ke Abeokuta a jihar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin gwamnan ta bangaren harkokin Musulunci, Wakeel Muslimeen ya ce akwai zargin wasu na kokarin kawo cikas a zanga-zangar.

Lawal ya ce wannan matsala da za a yi zanga-zanga kanta ba a iya Najeriya ba ne illa duniya baki daya duk akwai matsaloli.

Zanga-zanga: Malaman Musulunci sun ba matasa shawara

"Musabbabin wannan zanga-zanga ba iya Najeriya ba ne illa duniya baki daya, ya kamata mu kara hakuri kan haka."
"Shugabanni da Bola Tinubu da kuma gwamnanmu suna iya bakin kokarinsu wurin tabbatar shawo kan matsalolin."
"Bai kamata mu dauki tsauraran matakai ba wurin lalata kasa daya da muke da ita, da yardar Allah komai zai zama tarihi."

Kara karanta wannan

Ana fargabar tarzoma, lauya ya fadi hanyoyi 5 da za su samar da nasara a zanga zanga

- Wakeel Muslimeen

Malaman Musulunci sun zauna da Tinubu

Kun ji cewa Malaman addinin Musulunci sun samu zama da Shugaba Bola Tinubu kan halin kunci da ake ciki da zanga-zanga.

Malaman sun tabbatar da cewa sun bayyanawa Tinubu duka matsalolin da ake fuskanta inda ya yi musu alkawarin kawo karshensu.

Hakan bai rasa nasaba da shirin zanga-zanga da ake yi a fadin kasar baki daya inda wasu ke ganin za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.