Rundunar Ƴan Sanda Ta Tona Asiri, Ta Ce An Ɗauko Sojojin Haya a Zanga Zangar da Ake Shiryawa

Rundunar Ƴan Sanda Ta Tona Asiri, Ta Ce An Ɗauko Sojojin Haya a Zanga Zangar da Ake Shiryawa

  • Sufetan ƴan sanda na ƙasa ya bayyana cewa an shigo da sojojin haya daga ketare domin gurɓata zanga-zangar da ƴan Najeriya ke shirin yi
  • IGP Kayode Egbetokun ya gargaɗi matasa su guji shiga duk wani gungu da suka ci karo da shi a lokacin wannan zanga-zanga
  • Matasan Najeriya dai sun tsara fita kan tituna a faɗin ƙasar nan domin yin zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa da yunwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta gano cewa sojojin haya daga ƙasashen ketare na da hannu a zanga-zangar da matasa ke shirin yi a watan Agusta.

Sufeta Janar na rundunar ƴan sanda, IGP Kayode Egbetokun ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja yau Jumu'a, 26 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ba matasa damar zanga zanga, sun gindaya musu sharuda masu tsauri

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Sufetan ƴan sanda ya ce an shigo da sojojin haya daga ƙasar wajen a shirin zanga-zangar da za a yi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ya ce an ɗauko hayar ɓata gari daga ƙasashen ketare da zummar su gurɓata zanga-zangar kana su tayar da tarzoma a kasar nan, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Egbetokun ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan kuma su yi tunani sosai kafin su shiga kowace irin tawaga ta masu zanga-zanga.

Sufetan ya bayyana cewa rundunar ta bibiyi lamarin zanga-zangar kuma ta gano cewa wasu na son a yi ta cikin lumana yayin da wasu ke son su yi irin tashin-tashinar Kenya.

Zanga-zanga: Yadda aka shigo da sojojin haya

A rahoton Daily Trust, IGP Egbetokun ya ce:

"Tun farko mun sa ido kan barazanar wannan zanga zanga da ake shirin yi, wasu ƙungiyoyi sun nemi mutane su fito a tayar da tarzoma kamar abin da ya faru a ƙasar Kenya, wasu na ganin a yi zanga-zangar lumana.

Kara karanta wannan

"Ban da lalata kadarori": Tinubu ya fadi yadda ya shiga zanga zanga a lokacin soja

"Mun kuma lura da waɗanda suka nuna adawa da yin zanga-zanga a wannan lokacin saboda suna fargabar makiyan ƙasar nan ka iya amfani da damar su kawo tashin-tashina.
"Abin da suke tsoro gaskiya ne mun tabbatar da haka domin bayanan sirrin da muka samu sun nuna an shigo da sojojin haya daga ketare saboda su saje da ƴan zanga-zangar da ake shirin yi.

Jigon APC ya buƙaci janye zanga-zanga

A wani rahoton kuma Ƴan Najeriya sun samu shawara daga wajen babban jigo a jam'iyyar APC kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.

Uche Nwosu ya buƙaci matasan Najeriya da su haƙura da zanga-zangar sannan su ba Shugaba Bola Tinubu lokaci ya gyara ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262