Mai Neman Takaran Shugaban Kasa ya Dora Alhakin Zanga Zanga a kan Bola Tinubu
- A lokacin da kasar nan ta dauki kuwwar fita zanga-zanga daga farkon watan Agusta, an fara ganin gazawar shugaban kasa
- Mawallafin jaridar Ovation, Dele Momodu ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza fahimtar cewa Najeriya ba kamar jiha ba ce
- Ya shawarci shugaban kasar da ya gaggauta neman taimako daga wadanda su ka yi gwagwarmaya tare a baya a kan batun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Mawallafin jaridar Ovation, Dele Momodu ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da janyo zanga-zanga a kasar nan.
A wata doguwar wasika da ya rubuta ga shugaban kasar, Dele Momodu ya zargi Tinubu da gaza mulkar kasar nan duk da wahalar da 'yan kasa ke ciki.
A zungureriyar wasikar da ya wallafa a shafinsa na X, Dele Momodu ya kara da cewa 'yan Najeriya su na cikin wani hali, sai dai kalilan daga cikinsu shafaffu da mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bai kamata ka hana zanga-zanga ba," Momodu
Mawallafin jaridar Ovation ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na mulkin kasar nan kamar ya na mulkar jiha.
Mista Momodu ya ce kamata ya yi Tinubu, wanda aka rika yabawa da yadda ya mulki jihar Legas ya san cewa Najeriya kasa ce ba jiha ba, Jaridar Vanguard ta wallafa.
Ya ce abin takaici ne yadda Tinubu da aka sani da fafutukar ci gaban dimukuradiyya ne wanda ke hana jama'a zanga-zanga a yanzu.
"Tinubu ya nemi taimako kan zanga-zanga," Momodu
Mawallafin ya kara da shawartar shugaban kasa da ya gaggauta komawa wajen abokanansa da su ka yi fafutuka tare domin neman shawara a kan batun zanga-zanga.
Mista Momodu ya yi zargin wadanda ke ba wa Tinubu shawara a yanzu za su kai shi, su baro saboda son zuciyarsu kawai.
Zanga-zanga: 'Yan sanda sun dauki mataki
A baya mun kawo labarin cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana cewa ba za ta bari wasu su tayar da hargitsi yayin zanga-zangarda za a gudanar ba.
Rundunar ta ce za ta baza jami'anta 4,200 zuwa ko ina a fadin birnin tarayya Abuja domin dakile duk wani yunkurin tayar da hankula da kare lafiyar jama'ar birnin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng