Wani Abin Fashewa da Ake Zargin 'Bam' Ne Ya Tarwatse a Fitacciyar Kasuwa a Arewa
- Wani abun fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya tashi a kasuwar shanu da ke garin Buni Yadi a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe
- Rahotanni sun bayyana cewa bayan tashin bam ɗin, sojoji sun sake gano wani bam da aka dasa a kasuwar amma sun kwance shi
- Lamarin ya faru ne da tsakar rana yau Jumu'a kuma ya raunata wata yarinya, yanzu haka tana kwance a asibiti ana kula da lafiyarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Wani abin fashewa da ake kyautata zaton 'bam' ne ya tarwatse a babbar kasuwar Buni Yadi da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12.30 na tsakar rana yau Jumu'a, 26 ga watan Yuli, 2024.
Wani mazaunin garin Buni Yadi, Ali Alhassan ya shaidawa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho cewa tashin bam ɗin ya jikkata wata yarinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kwance bam a Yobe
Kakakin rundunar hadin gwiwa ta sashe na 2 na Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammad Shehu shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce sojoji sun sake gano wani ƙarin bam da aka dasa a kasuwar kuma sun yi nasarar kwance shi, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Ya kara da cewa a halin yanzu mutum daya da lamarin ya rutsa da shi yana kwance yana karbar magani a daya daga cikin asibitocin da ke Buni Yadi.
Kyaftin Muhammad Shehu ya yi ƙarin haske da cewa lamarin ya auku ne sakamakon dasa bam da aka yi a kasuwar ba wai harin ƙunar bakin wake ba ne.
Tashin bam ya lafa a jihar Yobe
Legit Hausa ta tattaro cewa Buni Yadi na da tazarar kilomita 54 daga Damaturu babban birnin jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabas.
Ita ce karamar hukumar da ta fi fama da hare-hare a jihar Yobe lokacin da mayakan Boko Haram suka ci karensu ba babbaka tsawon shekaru biyu.
Ƴan fashi sun baƙunci lahira a Abuja
A wani rahoton kuma yan sanda sun hallaka ƴan fashi biyu bayan sun kwato motar Jeep a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Alhamis.
Kwamishinan ƴan sandan babban birnin tarayya, CP Benneth Igweh ya ce sun kama ragowar ƴan fashin bayan musayar wuta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng