Zanga Zanga: Rundunar ’Yan Sanda Ta Dauki Mataki a Abuja, Ta Fadi Shirinta
- Rundunar 'yan sanda a birnin Tarayya Abuja ta tura jami'anta akalla 4,200 domin dakile miyagu da za su shiga zanga-zanga
- Rundunar ta ce za ta baza jami'anta lungu da sako na birnin domin kare lafiya da kuma dukiyoyin a'umma yayin zanga-zanga
- Mai magana da yawun 'yan sanda a birnin, Josephine Adeh ita ta bayyana haka inda ta ce sun shirya tsaf game da zanga-zangar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya, rundunar 'yan sanda ta dauki mataki a birnin Abuja.
Rundunar ta baza jami'anta 4,200 lungu da sakon birnin domin dakile tashin hankali yayin zanga-zangar da za a yi.
Zanga-zanga: An baza 'yan sanda a Abuja
Mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh ita ta bayyana haka a yau Juma'a 26 ga watan Yulin 2024, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kare rayuwa da kuma dukiyoyin al'umma saboda zargin shigar miyagu ciki.
Adeh ta ce za su kai samame wasu wurare na musamman ko kuma maboyar miyagu da hadin kan sauran jami'an tsaro a birnin, Punch ta tattaro.
"Rundunar 'yan sanda a Abuja ta baza jami'anta a birnin saboda shirin zanga-zanga game da halin kunci da ake ciki."
"Mun dauki matakin ne domin kare masu zanga-zanga da kuma dakile masu shirin kawo rigima a gwagwarmayar."
"An baza jami'ai da kuma kayan aiki lungu da sako a Abuja tare da binciken ababawan hawa da taimakon sauran jami'an tsaro."
- Josephine Adeh
Kwamishinan 'yan sanda ya yi gargadi
Kwamishinan 'yan sanda a Abuja, Benneth Igweh ya gargadi tada hankula da fashe-fashen dukiyoyin al'umma da na gwamnati inda ya ce ba za su lamunci haka ba.
CP ya yi kashedin ne a lokacin da ake shirin hawa tituna saboda a koka da matsin rayuwa.
Sultan, sarakunan gargajiya sun gana da Tinubu
Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya samu isa fadar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin wata ganawa.
Mai alfarma Sultan ya jagoranci sauran manyan sarakunan gargajiya a Najeriya domin ganawa a jiya Alhamis 25 ga watan Yulin 2024.
Asali: Legit.ng