"Tattalin Arzikin 2024 ya Ɗara na 2023 da Kaso Mai Tsoka" Inji Gwamnatin Tinubu

"Tattalin Arzikin 2024 ya Ɗara na 2023 da Kaso Mai Tsoka" Inji Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana wa 'yan Najeriya cewa tattalin arzikin kasar nan ya samu gagarumin ci gaba
  • Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka, inda ya ce a bangarori daban daban aka samu ci gaban
  • Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke shirin tsunduma zanga-zangar akwanaki 10 saboda matsin tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana samun gagarumin ci gaba ta fuskar habakar tattalin arzikin kasa saboda kudurorin da aka bijiro da su.

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ne ya bayyana haka a taron manema labarai a kan halin da tattalin arzikin kasa ke ciki a Abuja.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Wale Edun
Gwamnatin tarayya ta ce tattalin arziki ya habaka sosai Hoto: United APC
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Wale Edun ya bayyana cewa an samu gagarumin habakar arzikin kasa idan aka kwatanta da shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An samu ci gaban tattalin arziki," Edun

Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa habakar tattalin arzikin bana shi ne na biyu mafi girma a cikin shekaru shida.

Wannan batu na zuwa a lokacin da kasar na ke kukan babu, 'yan kasa kuma na cikin talauci.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Minista Edun ya ce an samu ci gaban arzikin a bangarorin noma, masana'antu da ayyuka.

Edun ya fadi dalilin habakar tattalin arziki

Mista Wale Edun ya bayyana cewa kudurorin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fitar ne su ka haddasa ci gaban da ake gani.

Ya ce an samu karuwar kudin shiga a bangaren fetur daga 11% a 2023 zuwa 30% a shekarar 2024, an kuma samu karuwar arziki a bangarorin da ba na fetur ba da 30% fiye da yadda aka yi hasashe.

Kara karanta wannan

Harkar noma: Gwamnatin Kano ta ware biliyoyi domin aikin madatsar ruwa

"Tattalin arziki ya kusa gyaruwa," Tinubu

A wani labarin kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce a kara hakuri, domin ana dab da samun habakar tattalin arziki yadda ake bukata.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne ga sarakunan gargajiya a kokarinsa na ganin sun wayar da kan jama'a domin kar su tsunduma zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.