Matasa na Shirin Zanga Zanga, Jami'an Tsaro Sun Harbe Yan Fashi Har Lahira

Matasa na Shirin Zanga Zanga, Jami'an Tsaro Sun Harbe Yan Fashi Har Lahira

  • Ƴan sanda sun hallaka ƴan fashi biyu bayan sun kwato motar Jeep a babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Alhamis
  • Kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh ya ce sun kama ragowar ƴan fashin bayan musayar wuta
  • Ya ce waɗanda suka kama sun taimaka masu da bayanai wajen kwato wata ƙarin motar da suka sata daga wani mazaunin yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an tsaro sun bindige ƴan fashi da makami biyu har lahira yayin da suka yi ƙoƙarin satar mota Prado Jeep a yankin Jahi da ke birnin Abuja.

Kwamishinan ƴan sandan Abuja, CP Benneth Igweh ne ya sanar da haka ga manema labarai yayin nuna ragowar ƴan fashin da aka kama ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

An kashe mutane yayin da rigimar sarauta ta ƙara tsanani, hadimin gwamna ya yi magana

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sanda sun harbe ƴan fashi da makami har lahira a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:45 na daren jiya Alhamis lokacin da ƴan fashin suka yi musayar wuta da dakarun ƴan sanda, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abuja: Ƴan sanda sun rutsa ƴan fashi

CP Igweh ya ce ƴan fashin su huɗu sun buɗewa tawagar ƴan sanda karkashin DPO na Mabushi wuta, lamarin da ya kai ga muyar wuta a tsakaninsu.

Ya ce nan take ƴan sanda suka yi nasarar harbe biyu daga ciki har lahira kana suka damƙe ragowar mutum biyun bisa zargin aikata laifin fashi a makami.

Kwamishinan ƴan sandan ya ce:

"Yayin musayar wuta da jami'an ƴan sanda, mun kama mutum biyu daga cikin ƴan fashin, Joshua Godfrey da ake kira Dogo da Abdulrahaman Mamuda duk daga ƙauyen Mabushi."

Ƴan sanda sun kwato motoci

Bugu da ƙari CP Benneth Igweh ya bayyana cewa ƴan sanda sun kwato motar aiki Toyota Matrix mai lamba BWR 626 JB daga hannun ƴan fashin, Daily Post ta kawo.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya dauki zafi kan zanga zanga, ya fadi dalilin shiryata

Igweh ya ce wadanda aka kama sun jagoranci jami’an ‘yan sanda wajen kwato wata mota kirar Toyota Corolla mai lamba RBC 743 AH, da suka kwata daga wani mazaunin yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya jaddada kudirin rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma kana ya roki mazauna su yi taka tsan-tsan, su sanar da ƴan sanda duk abin da suke zargi.

Yan bindiga sun kashe basarake a Taraba

A wani rahoton kuma yan bindiga sun kai farmaki kan titin Takum zuwa Chanchangi, sun halaka basarake da ɗansa ranar Jumu'a da yamma a jihar Taraba.

Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262