“Mayu Ne Sila": Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Watannin da Ya Yi a Cikin Mahaifiyarsa

“Mayu Ne Sila": Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Watannin da Ya Yi a Cikin Mahaifiyarsa

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya ya nuna damuwa kan yadda mahaifiyarsa ba ta ci ribar daukar nauyinsa da ta yi ba a baya
  • Obasanjo ya ce an fada masa cewa mahaifiyarsa ta dauki nauyinsa a cikinta har na tsawon watanni 12 kafin ta haife shi
  • Ya ce hakan bai rasa nasaba da wahalar da mayu suka ba ta wanda idan ba domin taimakon ubangiji ba da ba za ta haihu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana kalubale da ya fuskanta kafin zuwansa duniya.

Obasanjo ya ce mahaifiyarsa, Bernice Obasanjo ta dauki nauyinsa a cikinta har na tsawon watanni 12 kafin ta haife shi.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Obasanjo ya yi magana kan wahalar da mahaifiyarsa ta sha game da cikinsa
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya fadi watannin da ya shafe a cikin mahaifiyarsa. Hoto: Riccardo Savi.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya bayyana wahalar da ya sha

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Kahinde Akinyemi ya fitar a Abeokuta da ke jihar Ogun, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya alakanta wahalar da mahaifiyarsa ta sha da matsalolin mayu na tsawon watanni kafin samun taimakon ubangiji.

Tsohon shugaban kasa ya koka kan yadda mahaifiyarsa ba ta samu tsawon rai ba domin ganin yadda ya cimma nasara a rayuwa, Leadership ta tattaro.

Yadda Obasanjo ya shafe watanni a ciki

"An fada mani cewa na kasance a cikin mahaifiyata har na tsawon watanni 12 , tun bayan haihuwata take cigaba da kula da ni."
"Tana da yara har guda tara, amma mu biyu ne kawai muka rayu da ni da kuma wata 'yar uwata."
"Ni kadai ne na je makaranta saboda mahaifina ya yi imanin cewa duk yadda mace ta yi ilimi za ta kare ne a madafi."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya amince da kafa hukumar cigaban jihohin Arewacin Najeriya

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya yabawa basarake kan taimakonsa

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yabawa tsohon Sarkin Adamawa kan taimkonsa a gidan yari.

Obasanjo ya ce yaki amincewa da bukatar taimakon daga basaraken saboda bai son ya saba da dadi a gidan yari a lokacin domin sanin rayuwa.

Tsohon shugaban Najeriyan ya ce zamansa a gidan kaso ya sauya masa rayuwa tare da tasiri wurin inganta Najeriya bayan ya zama shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.