Kungiyar TUC ta Tsame Kanta Daga Zanga Zanga, Ta Turawa Jami'an Tsaro Sako

Kungiyar TUC ta Tsame Kanta Daga Zanga Zanga, Ta Turawa Jami'an Tsaro Sako

  • Kungiyar 'yan kasuwa ta kasa (TUC) ta ce ba ta daga cikin wadanda su ka yi gangamin hada zanga-zangar gama gari
  • 'Yan Njaeriya da talauci ya addabe su sun daura aniyar nuna bacin ransu ta hanyar zanga-zanga daga farkon watan Agusta
  • Shugaban kungoyar TUC, Festus Osifo ya bayyana cewa dole hukumomin tsaron kasar nan su ba su kariya kamar yadda doka ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Biyo bayan kara daura damarar fita zanga-zanga da 'yan kasa ke yi, kungiyar 'yan kasuwa (TUC) ta nemi a ba wa masu fitowa tsaro.

Shugaban kungiyar na kasa, Festus Osifo ya ce dokar kasa ta dora alhakin tabbatar da tsare rayukan jama'a a hannun jami'an tsaro a lokacin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar matasan Najeriya ta tura sako zuwa ga rassanta 104

Festus
TUC ta nemi jami'an tsaro su ba wa masu zanga-zanga kariya Hoto: NILDS
Asali: Facebook

Channels Television ta tattaro cewa TUC na ganin samar da tsaron zai kawar da kutsen miyagun mutane wajen tayar da fitina a lokacin zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"TUC ba ta kira zanga zanga ba," Osifo

Kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta ce ba ta kira kowa ya fito zanga-zanga ba a gangamin da 'yan kasa ke ci gaba da hadawa a halin yanzu.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ne ya bayyana haka, inda ya ce amma dokar kasa ta ba wa jama'a damar fitowa zanga-zangar lumana.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa shugaban TUC ya bayyana farin ciki a kan yadda su ke samun tabbacin za a ba wa masu zanga-zanga kariya.

Ya kara jaddada kira ga dukkanin jami'an tsaron kasar nan kan a samar da tsaro sannan a tabbatar bata-gari ba su shiga cikin masu zanga-zanga ba.

Kara karanta wannan

"Ba mu san dalilinku ba:" Gwamnonin APC sun tura sako ga matasa kan zanga-zanga

Zanga-zanga: Matasa za su fadi matsayarta

A baya mun kawo labarin cewa kungiyar matasan Najeriya (NYCN) ta ce za ta fadi matsayarta a kan shirin fita zanga-zanga daga ranar 1 Agusta, 2024.

Shugaban kungiyar na kasa, Sukubo Sara-Igbe Sukubo ya ce sun tattauna da sauran shugabannin jihohi, kuma za su bayyana matsayarsu ranar 31 Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.