Bayan Ganawa da Tinubu, Malaman Izala da Ɗariƙa Sun Faɗi Matsaya Kan Zanga Zanga

Bayan Ganawa da Tinubu, Malaman Izala da Ɗariƙa Sun Faɗi Matsaya Kan Zanga Zanga

  • Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun isar da koken talakawa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Villa ranar Alhamis
  • Bayan ganawa da Tinubu, malaman sun roƙi ƴan Najeriya musamman matasa su haƙura sun janye zanga-zangar da suke shirin yi a watan Agusta
  • Shugaban Izala kuma jagoran tawagar malaman da suka gana da Tinubu, Abdullahi Bala Lau ya roƙi Musulmi da Kirista su taya Tinubu da addu'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Manyan Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun yi kira ga matasa su janye zanga-zangar da suka shirya yi a watan Agusta da ke tafe.

Malumman na Ɗarika da Izala sun bayyana haka ne bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Villa ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

A kara hakuri, tattalin arziki na dab da gyaruwa: Abin da Tinubu ya fadawa sarakuna

Malaman Musulunci da Bola Tinubu.
Malamai sun roki matasa su janye zanga-zangar da suke shirin yi a Najeriya Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu ya gana da malamai da sarakuna

Premium Times ta ce Tinubu ya yi ganawa daban-daban ranar Alhamis da gwamnonin APC, sarakunan gargajiya daga sassan kasar nan da malaman addinin Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarukan dai wani bangare ne na kokarin dakile karya doka da oda a daidai lokacin da matasan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar.

Malamai sun isar da saƙon ƴan Najeriya

Bayan ganawar da Tinubu, jagoran tawagar malamai kuma shugaban Izala (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce sun mika koken jama'a ga shugaban Najeriya.

"Kamar yadda kuka sani, mu talakawa ke kawo ma kokensu kuma Alhamdulillah mun haɗa duk abin da mutane ke cewa game da tsadar rayuwa, rashin tsaro mun isar da saƙon ga shugaban ƙasa.
"Shugaban ƙasa ya tarbe mu hannu bibbiyu kuma ya yaba mana kan abin da ya kawo mu da abubuwan da muka isar masa sannan ya yi alƙawarin zai magance su."

Kara karanta wannan

"A rungumi zaman lafiya": Malam Izala da Darika sun yi magana bayan ganawa da Tinubu

- Sheikh Bala Lau.

Daga nan sai babban malamin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da Musulmi da Kirista da su ƙara hakuri da kuma yi wa shugaban kasa addu’a, kamar yadda Arise tv ta tattaro.

"Muna kira ga ’yan Najeriya Musulmi da Kirista su yi hakuri, idan Allah ya so za su ga sakamako nan ba da jimawa ba," in ji shi.

Abin da Tinubu ya faɗawa sarakuna

Kuna da labarin Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa yana aiki tukuru domin farfado da tattalin arzikin kasar, kuma ana samun nasara.

Shugaban kasar wanda ya yarda cewa akwai matsin rayuwa a kasar ya ce tattalin arzikin Najeriya na hanyar farfadowa sannu a hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262