Kabilar Ibo Sun Yi Rashi Bayan Rasuwar Shugaban Ohanaeze Ndigbo, Bayanai Sun Fito
- Kabilar Igbo ta shiga cikin jimami da dimuwa bayan rasuwar shugabanta na kasa baki daya, Cif Emmanuel Iwuanyanwu
- Iyalan marigayin sun sanar da rasuwar Iwuanyanwu ne a yau Alhamis 25 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya
- Marigayin wanda fitaccen dan kasuwa ne kuma mai kamfanin jaridar Champion ya rasu yana da shekaru 82 a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndigbo kuma fitaccen dan kasuwa, Cif Emmanuel Iwuanyanwu ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 25 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da gajeruwar jinya yana da shekaru 82 a duniya.
Iwuanyanwu: Iyalan marigayin sun fitar da sanarwa
Dan marigayin mai suna, Jude Iwuanyanwu shi ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa a cikin wata sanarwa, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin ya yi suna a shugabancin kungiyar kabilar Igbo inda ya rike shugabancin kungiyar Owerri Peoples Assembly kafin rasuwarsa.
Iwuanyanwu ya rasu ya bar matarsa guda daya mai suna Princess Frances Iwuanyanwu da kuma yara da jikoki da dama, Punch ta tattaro.
Rahotanni sun tabbatar da cewa iyaan marigayin za su sanar da shirye-shiryen bikin binne Iwuanyanwu nan ba da jimawa ba.
Yaushe Iwuanyanwu ya samu shugabancin Ohanaeze Ndigbo?
Iwuanyanwu ya dare shugabancin kungiyar a watan Janairun 2021 a babban taron kungiyar da aka yi a birnin Owerri da ke jihar Imo.
Marigayin ya maye gurbin Cif Nnia Nwodo ne bayan yarjejeniyar da aka yi da zabensa ba tare da hamayya ba inda ya kawo sauye-sauye a kungiyar da dama.
Ohanaeze Ndigbo ta magantu kan rashin tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Ƙungiyar zamantakewa da al'ada ta Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta ce Najeriya ba za ta samu zaman lafiya da cigaba ba.
Mai magana da yawun ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Chiedozie Ogbonnia, ya bayyana haka inda ya ce ana nunawa Igbo rashin adalci.
Ogbonnia ya tuna lokacin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a watan Janairun 2021 ya naɗa hafsoshin tsaro amma babu ɗan ƙabilar Ibo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng