Bayan Tinubu Ya Gana da Manyan Kasa, Kungiyar Addini Ta Barranta Daga Zanga Zanga

Bayan Tinubu Ya Gana da Manyan Kasa, Kungiyar Addini Ta Barranta Daga Zanga Zanga

  • Al'ummar Najeriya na cigaba da tattaunawa kan zanga zanga da ake shirin yi a ranar 1 ga watan Agustan nan mai kamawa
  • Yan cocin ECWA sun yi gardagi ga al'umma kan rashin amfanin shiga zanga zangar saboda tsoron barkewar rikici a faɗin Najeriya
  • Jami'in yada labaran ECWA, Rabaran Ibrahim Kassim ya bayyana ƙoƙarin da suke yi wajen ganin an samu sauƙin rayuwa a kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Cocin ECWA a jihar Filato ya bayyana matsayarsa kan zanga zanga da ake shirin yi a faɗin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa jami'in yada labaran cocin, Rabaran Ibrahim Kassim ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Ana fargabar tarzoma, lauya ya fadi hanyoyi 5 da za su samar da nasara a zanga zanga

Cocin ECWA
Cocin ECWA ya bukaci matasa su hakura da zanga zanga. Hoto: ECWA Goodnews Church, Jos
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Rabaran Ibrahim Kassim ya fadi matakan da suke dauka maimakon zanga zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kin shigar ECWA zanga zanga

Rabaran Ibrahim Kassim ya bayyana cewa suna tsoron zanga zangar ta barke ta dawo tarzoma kamar yadda ya faru a lokacin End SARS.

Malamin ya ce abu ne mai sauki a Najeriya a samu bata gari su yi rinjaye a kan tayar da fitina a lokacin zanga zanga da aka nufi lumuna da ita.

Cocin ECWA ta yi kira ga ƴaƴanta

Har ila yau, Rabaran Ibrahim Kassim ya yi kira da dukkan masu zuwa cocin ECWA da su nisanci zanga zangar.

Ya kuma kara da cewa suna tabbatarwa duniya sun barranta da zanga zangar da masu shirya ta a Najeriya.

Tsadar rayuwa: Kokarin da ECWA ke yi

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero mutanen da ake shirin kai wa hari a lokacin zanga zanga

Daily Post ta wallafa cewa Rabaran Ibrahim Kassim ya bayyana cewa suna sane da halin kuncin rayuwa da ake ciki a Najeriya a halin yanzu.

Amma a karkashin haka suna daukan matakin ba gwamnatoci shawara domin ganin a samu sauƙin rayuwa.

Tinubu ya kira gwamnoni kan anga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyato gwamnonin jam'iyyar APC domin tattaunawa a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Bola Tinubu ya sanya labule da gwamnonin jihohin ne yayin da matasa ke ci gaba da shirin fitowa kan tituna domin yin zanga-zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng