Sarakuna Sun Shiga Uku, an Bukaci Gwamna Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kansu
- Yayin da ake zargin sarakuna da boye miyagu a yankunansu, matasa a jihar Ondo sun ba Gwamna Lucky Aiyedatiwa shawara
- Matasan karkashin kungiyar Indigenous Youth Leaders sun bukaci ya hukunta duk basaraken da aka samu da aikata haka
- Matasan sun nuna a shirye suke domin ba gwamnati duka goyon bayan wurin yaki da hakan a fadin jihar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Wasu matasa a jihar Ondo sun bukaci Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya hukunta wasu daga cikin sarakuna.
Kungiyar Indigenous Youth Leaders ta bukaci gwamnan ya hukunta sarakuna da ke daurewa masu aikata laifuka gindi.
Ondo: Matasa sun ba gwamna shawara
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a bangaren matasa da samar da aikin yi ya fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun bayyana shirinsu na goyon bayan gwamnatin jihar da jami'an tsaro domin yakar masu aikata laifuka.
Sun bayyana irin gudunmawar da sarakunan gargajiya za su bayar wurin tabbatar da dakile miyagu a yankunansu, Vanguard ta tattaro.
Matasan sun yi barazana ga sarakunan Ondo
"Duk wani basarake da aka samu da laifin boye masu laifi ko ba da wata dama gare su zai fuskanci hukunci mai tsanani."
"Muna kira da gwamnati ta ba sarakunan goyon baya domin yin aiki kafada da kafada da matasa wurin kare yankunansu."
"Muna Allah wadai da yawan shaye-shaye da safarar kwayoyi a jihar tare gargadin masu yin haka su tuba ko kuma su bar jihar baki daya."
- Cewar matasan
Hakan bai rasa nasaba da yawan samun miyagu a yankuna daban-daban da sarakunan ke wakilta da ake zargin suna sane da su.
Gwamna Makinde ya magantu kan dokar masarautu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi martani kan hayarniyar da ake yi game da dokar masarautu a jihar.
Makinde ya nuna damuwa kan yadda ake yada jita-jitar cewa dokar na neman dakile gadon kujerar sarautar Olubadan a gaba.
An yi yada jita-jitar a lokacin bikin nadin sarautar sabon sarkin Ibadan da ake kira Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng