Ana Fargabar Tarzoma, Lauya Ya Fadi Hanyoyi 5 da Za Su Samar da Nasara a Zanga Zanga

Ana Fargabar Tarzoma, Lauya Ya Fadi Hanyoyi 5 da Za Su Samar da Nasara a Zanga Zanga

  • Magana kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa na kara jan hankulan al'umma da shugabanni a fadin Najeriya
  • Hukumomi da malaman addini sun nuna fargaba kan cewa zanga zangar za ta iya haifar da tarzoma a fadin ƙasar nan
  • Lauya mai fashin baki, Dr. Audu Bulama Bukarti ya bayyana hanyoyi biyar da za a bi wajen samun nasara a zanga zangar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Maganar zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya na cigaba da daukan hankulan al'umma.

Dakta Audu Bulama Bukarti ya lissafa hanyoyi biyar da za a bi wajen kaucewa tayar da riciki a lokacin zanga zangar.

Kara karanta wannan

Wasu matasan Arewa sun fadi sharuda 3 kafin janye zanga zangar da aka shirya

Audu Bulama Bukarti
Lauya ya fadi hanyoyin samun nasara a zanga zanga. Hoto: Audu Bulama Bukarti.
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da Dakta Audu Bulama Bukarti ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hanyoyin samun nasara a anga zanga

  1. Lauya mai fashin baki, Dakta Audu Bulama Bukarti ya ce mataki farko shi ne a samu shugaba da zai jagoranci zanga zangar.
  2. Dakta Audu Bulama ya ce yana da muhimmanci masu zanga zangar su lissafa abin da suke buƙata a wajen gwamantin tarayya.
  3. Lauyan ya kara da cewa dole musu zanga zangar su tabbatar ba a taba kayan mutane ba ko kuma kona kayan gwamnati.
  4. Dakta Bulama ya ce akwai bukatar a ware ranaku da za a rika yin zanga zangar domin mutane su samu damar yin ayyuka a sauran kwanakin.
  5. A karshe, lauyan ya ce dole masu zanga zangar su hakura da zarar gwamanti ta amince da biya musu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta gamu da cikas, dalibai sun janye jiki

Dakta Audu Bulama Bukarti ya ce matuƙar aka bi waɗannan hanyoyi to za a samu nasara a yayin zanga zangar.

Za a rufe asibitocin Bauchi yayin zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi karkashin Sanata Bala Muhammad ta fara shiri yayin da matasa ke yunkurin fara zanga zanga a Najeriya.

Ma'aikatar lafiya a jihar Bauchi ta yi bayani kan yadda za ta fuskanci ranar zanga zangar da matasan Najeriya ke shirin farawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng