Zanga Zanga: Jigon APC Ya Fadi Abin da 'Yan Najeriya Ya Kamata Su Yi Wa Tinubu
- Ƴan Najeriya sun samu shawara daga wajen babban jigo a jam'iyyar APC kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar
- Uche Nwosu ya buƙaci matasan Najeriya da su haƙura da zanga-zangar sannan su ba Shugaba Bola Tinubu lokaci ya gyara ƙasar nan
- Ya bayyana cewa shekara ɗaya da Tinubu ya yi a kan mulki, ta yi kaɗan ya gyara ɓarnar da aka kwashe shekaru ana yi a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar APC, Uche Nwosu, ya roƙi ƴan Najeriya da su ba Shugaba Bola Tinubu lokaci tare da fasa yin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Uche Nwosu ya bayyana cewa babu adalci ko kaɗan a yi tsammanin cewa gwamnatin da ta yi shekara ɗaya a kan mulki za ta gyara ɓarnar da aka kwashe shekaru ana yi a ƙasar nan.
"A yi wa Tinubu uzuri" - Jigon APC
Tsohon shugaban ma'aikatan na tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Alhamis, cewar jaridar PM News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na jam'iyyar APC ya nuna cewa ya kamata a yi wa Shugaba Tinubu uzuri, a ba shi lokaci ya gyara ɓarnar da aka yi a ƙasar nan.
Ya bayyana cewa tabbas wasu tsare-tsaren gwamnatin Tinubu sun yi tsauri a yanzu, amma za a ci moriyarsu a nan gaba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Wane kira ya yi kan zanga-zanga?
"Ina amfani da wannan damar domin kira ga matasanmu da su rungumi zaman lafiya. Tabbas muna cikin lokaci mai wuya a matsayinmu na ƙasa. Amma kada mu zama waɗanda gwiwoyinsu suka sare."
"Tabbas a dimokuraɗiyya ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga amma mafi yawan zanga-zangar da ake yi a Najeriya inda muke da sama da ƙaɓila 250, ba a gama su lafiya."
"Misali a lokacin zanga-zangar lumana ta EndSARS wasu ɓaragurbi sun yi kutse cikinta inda aka lalata kadarori na miliyoyin Naira tare da asarar rayuka masu yawa."
- Uche Nwosu
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
Gwamnatin Tinubu ta bayyana dalilin da ya sa ba ta son a yi zanga-zanga
Ana harin zanga-zanga, Sufeto Janar na ƴan sanda ya aika da saƙo mai zafi
Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi
Babu batun zanga-zanga a Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ba za a yi zanga-zanga a jihar ta yankin Arewa maso Gabas din ba.
Gwamnatin jihar ta kuma gargaɗi masu shirin gudanar da zanga-zangar da su shiga taitayinsu sannan su sake tunani domin ba za ta lamunci hakan ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng