Hedkwatar Tsaro Ta Jero Mutanen da Ake Shirin Kai Wa Hari a Lokacin Zanga Zanga
- Hedkwatar tsaro ta gargaɗi yan Najeriya su yi taka tsan-tsan a lokacin zanga-zangar da aka shirya yi a watan da ke tafe
- Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya jero rukunin mutanen da wasu ɓata gari ke shirin faramaki yayin zanga-zangar
- Wannan na zuwa ne yayin da matasa suka tsara gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hedktwar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa ta gano wani shiri da ɓata-gari ke yi na kai farmaki kan wasu mutane a lokacin zanga-zangar da za a yi.
Mai magana da yawun DHQ na kasa, Manjo Janar Edward Buba ne ya faɗi haka a taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce hedkwatar tsaro ta bankaɗo shirin wasu bara gurbi na kai hari kan masu wayoyin hannu, gidaje da masu motoci a lokacin zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Channels tv ta tattaro cewa ƴan Najeriya musamman matasa na shirin fita zanga-zanga kan yunwa da tsadar rayuwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
DHQ ta jero waɗanda ke cikin haɗari
Da yake jero waɗanda suka gano ana shirin farmaka a lokacin wannan zanga-zanga, Janar Buba ya ce:
"Mun riga mun gano shirin wasu ɓata gari da za su shiga zanga-zangar da aka shirya domin tada zaune tsaye, mafi akasarin mutane ba su san wannan makircin ba.
"Alal misali, alamu sun nuna idan kana da wayar hannu, ko kana da mota ko shago gida ko masuburbuɗar sanyi (AC) to kana cikin abin harin ɓata gari a zanga zangar."
Bugu da ƙari, ya yi kashedi ga masu shirin fitowa wannan zanga-zanga su kauce wa duk wani abu da zai haifar da tashin hankali, The Nation ta ruwaito.
Gwamnatin Bauchi ta magantu kan zanga-zanga
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Bauchi ta fito ta bayyana matsayarta kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Kashim, ya bayyana cewa babu wata zanga-zanga da za a gudanar a Bauchi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng