Zanga Zanga: Dan Takarar Shugaban Kasa ya Gindayawa Masu Shirin Fita Sharadi

Zanga Zanga: Dan Takarar Shugaban Kasa ya Gindayawa Masu Shirin Fita Sharadi

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Faduri Oluwadare Joseph ya karfafawa matasan kasar nan gwiwa game da fita zanga-zanga
  • Amma dan takarar shugaban kasar ya ce su kiyaye saboda gudun gurbacewar manufarsu daga lumana zuwa tashin hankali
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da rundunar sojoji ta bayyana cewa ta samu bayanai a kan wani mugun kulli game da zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Matasan kasar nan da sauran masu shirin fita zanga-zanga sun kara samun karfin gwiwa daga tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Faduri Oluwadare Joseph.

Kwamred Faduri Oluwadare Joseph ya bayyana cewa ai 'yan Najeriya sun yi hakuri, domin tun a baya ya kamata jama'ar kasar nan su fito nuna bacin ransu a kan halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar matasan Najeriya ta tura sako zuwa ga rassanta 104

Zanga Zanga
Dan takarar shugaban kasa ya shawarci masu shirin zanga-zanga su kula da bata-gari Hoto: Nur Photo
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta tattara cewa dan takarar shugaban kasar ya shawarci matasa a kan lallai su kula da bata gari da za su iya shiga cikinsu domin tayar da hankula.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta bari a yi zanga-zanga," Joseph

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Faduri Oluwadare Joseph ya shawarci gwamnatin tarayya ta bari 'yan kasa su bayyana abin da ke ransu, The Nation ta wallafa.

Dan takarar na wannan batu ne a lokacin da gwamnatocin kasar nan ke ta kiraye-kiraye a kan gujewa shiga zanga-zanga saboda illarsa ga kasa.

Ya ce hurumin 'yan Najeriya ne su tabbata bata gari ba su yi amfani da su wajen tayar da hankulan jama'a da ka iya haddasa asarar rayuka ba.

Sojoji sun gano matsala a shirin zanga-zanga

A wani labarin kuma rundunar sojojin Najeriya ta bayyana bankado wani kullallen shiri da ake sa ran wasu bata-gari za su yi yayin zanga-zangar gama gari da za a fara daga 1 Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

"Ba mu san dalilinku ba:" Gwamnonin APC sun tura sako ga matasa kan zanga-zanga

Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba da ya bayyana haka ya ce ba za su lamunci haka ba, domin sun shirya tsaf domin tunkarar shirin da ake na tayar da zaune tsaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.