Akpabio Ya Yi Kuskure, Akwai Ma’aikatan da Ba Za Su Samu Albashin N70,000 Ba
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tafka kuskure yayin da yake jawabi kan sabon mafi karancin albashi
- Akpabio ya yi ikirarin cewa sabon albashin ya shafi duk kananan ma'aikata ciki har da masu aikatau da gadi a gidaje
- Sai dai kuma sabanin bayanin Akpabio, kwata-kwata sabon kudirin mafi karancin albashin ba haka yake nufi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - A ranar Talata 23 ga watan Yulin 2024 Majalisun Tarayya suka amince da kudirin sabon mafi karancin albashi a Najeriya.
Kudirin ya tsallake karatu na daya da biyu da kuma uku a cikin awa daya kacal a duka Majalisun Tarayya da ake da su.
Jawabin Akpabio da ya tayar da kura
Daga cikin gyaran fuska da aka yi a kudirin akwai karin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 da kuma sabunta abashin duk shekaru uku, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce duk wanda ya dauko mai gadi ko 'yar aiki dole sai ya biya su N70,000.
Sai dai Akpabio ya sha suka daga 'yan Najeriya inda suke tunanin anya kuwa ya san mene ke kunshe a cikin dokar da aka amince da ita.
Martanin wasu kan jawabin Akpabio:
Tohluh Briggs:
"Wannan shi ne mafi girman barkwanci, ya kamata ka sake duba dokokin da ke tattare da mafi karancin albashi."
Philemon Kuza:
"Da gaske? mene ya faru? mene kuma ya sauya a dokar?"
Saboda a cikin kudirin akwai wasu jerin ma'aikata da ba za su samu karin mafi karancin albashin N70,000 da aka tabbatar ba, cewar TheCable.
Daga sashe na 3 (1) na dokar shi ne duk wata ma'aikata ko kamfani za su biya ma'aikatanta mafi karancin albashin N70,000.
Wadanda za su samu albashin N70,000
Amma kuma ban da ma'aikata ko kamfani da ke da ma'aikata kasa da 25 kamar yadda sashe na hudu na dokar ya fayyace.
Sauran da ba za su samu albashin N70,000 sun hada da masu aikin wucin gadi da wadanda ke biyan kudin aiki adadin aikin da mutum ya yi.
Sai kuma wadanda ke aiki ba na kullum ba ko na lokaci zuwa lokaci kamar masu aikin gona da sauransu.
Gwamnoni sun rude kan mafi karancin albashi
Kun ji cewa wasu gwamnonin jihohin Najeriya da dama sun ki yin martani kan sabon mafi karancin albashin N70,000.
Duk da haka wasu gwamnoni sun sha alwashin biyan albashin yayin da wasu suke jiran ganawar kungiyar gwamnoni ta NGF.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng