Gwamnonin Jihohi 36 Sun Yi Magana Kan Zanga Zangar da Matasa Ke Shirin Yi
- A karshe dai gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga-zangar da matasa ke shirin yi a watan Agusta mai zuwa
- Gwamnonin sun bayyana cewa sun samu bayani daga ofishin Nuhu Ribadu kan zanga zanga kuma ya yi alƙawarin taimaka masu wajen samar da tsaro
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da laluben mafita kan zanga-zangar da ake shirin yi a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi magana kan al'amuran tsaro musamman zanga-zangar da matasa ke shirin yi a watan Agusta.
Ƙungiyar ta bayyana cewa bayanan da ta samu daga ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa (NSA) sun nuna damuwar da ake ciki game da zanga-zangar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da NGF ta wallafa a shafinta na X bayan taron gwamnonin 36 karkashin gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin sun gana ne a sakatariyar kungiyar NGF da ke birnin tarayya Abuja a daren jiya Laraba, 24 ga wstan Yuli, 2024.
Wane mataki gwamnoni suka ɗauka?
Sanarwar ta ce mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya yi alƙawarin taimakawa gwamnoni wajen inganta tsaro a jihohinsu.
Wani sashen sanarwar ya ce:
"Kungiyar gwamnoni ta samu karin bayani daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) kan halin da ake ciki game da tsaro a kasar nan
."Ya gaya mana halin da ake ciki game da shirin da matasa ke yi na gudanar da zanga-zanga domin jan hankalin gwamnati. NSA ya yi alƙawarin taimakawa gwamnoni wajen inganta tsaro a yankunansu."
"Gwamnonin sun godewa mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro kana suka jaddada kudirin su na inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a matakin jihohi."
Gwamnoni za su gana da ministoci
A wani rahoton kun ji cewa Gwamnonin jihohin Najeriya da wasu ministoci za su gana da nufin lalubo hanyar hana faruwar zanga-zangar da matasa ke shirin yi.
Hakan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauki a taron George Akume da duka ministoci ranar Laraba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng