Gwamnoni Sun Shiga Taro a Abuja Ana Shirin Zanga Zanga, An Gano Abubuwa 3

Gwamnoni Sun Shiga Taro a Abuja Ana Shirin Zanga Zanga, An Gano Abubuwa 3

  • Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta kira taro na musamman a daidai lokacin da matasa ke shirin yin zanga-zanga
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnoni sun isa sakatariyar NGF da ke birnin Abuja kuma ana sa za su tattauna kan abubuwa
  • Wannan ne karo na farko da gwamnonin ke gudanar da taro tun bayan cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa gwamnoni daga duka jihohin Najeriya na gudanar da taro na musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnonin ƙarƙashin inuwar ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) na gudanar da taron ne a sakatariyar NGF da ke birnin tarayya.

Gwamnonin jihohi 36.
Gwamnonin Najeriya sun shiga taro a birnin tarayya Abuja Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Facebook

Channels tv ta tatttaro cewa tuni wasu gwamnoni suka isa ɗakin taron ciki har da gwamnan Bauchi kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin da suka halarci taron

Sauran waɗanda aka ga zuwansu sun haɗa da Dauda Lawal na jihar Zamfara Caleb Mutfwang na jihar Filato, Sheriff Oborevwori na Delta da Alex Otti na jihar Abia.

Gwamnonin jihohin Enugu, Peter Mbah da Borno, Farfesa Babagana Zulum, sun tura mataimakansu domin su wakilce su.

Har kawo yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton, ba a fitar da maƙasudin taron a hukumance ba.

Abubuwa 3 da NGF za ta tattauna

Sai dai idan za ku iya tunawa a taronsu na ƙarshe, gwamnonin sun yi wa ma'aikata alƙawarin biyansu albashi daidai gwargwado.

Haka nan wannan shi ne taron gwamnoni na farko tun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Don haka ana tunanin za su tattauna kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya kuma su fitar da matsayinsu kan N70,000 da aka amince da ita.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da wasu ministoci sun fara koƙarin hana matasa zanga zangar da suke shirin yi

Bugu da ƙari da yiwuwar gwamnonin su yi magana kan zanga-zangar da matasan Najeriya ke shirin yi a watan Agusta mai zuwa inji Tribune Nigeria.

Har ila yau, ana tsammani gwamnonin za su faɗi matsayarsu a kungiyance kan hukuncin kotun koli na baiwa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu.

Sarkin Benin ya roƙi matasa abu 1

Kun ji cewa Sarkin Benin, Oba Ewaure II ya yi kira ga matasan Najeriya su janye zanga-zangar da suka shirya yi ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Basaraken ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsaren da ake sa ran za su share hawayen ƴan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262