An Shiga Jimami Bayan Mutuwar Fitaccen Basarake Mai Daraja, Ya Yi Shura
- Al'ummar jihar Oyo sun shiga dimuwa bayan sanar da rasuwar mai sarautar gargajiya, Oba Lateef Gbadamosi Adebimpe
- Basaraken da ake kira Osi Balogun na Ibadanland ya rasa ransa ne a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya
- Marigayin kafin rasuwarsa ya kasance daga cikin sarakuna kalilan da suka samu damar samun darajar zama Oba a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - An shiga tashin hankali bayan rasuwar fitaccen basarake a jihar Oyo, Oba Lateef Gbadamosi Adebimpe.
Basaraken, Osi Balogun na Ibadanland ya rasu ne a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024 bayan ya sha fama da jinya.
Oyo: Osi Balogun a Ibadanland ya rasu
Sai dai har zuwa tattara wannan rahoton ba a samu karin bayani kan mutuwar basaraken ba, kamar yadda Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basaraken kafin rasuwarsa ya wakilci Olubadan, Oba Akinyole Owolabi Olakulehin a bikin bude sabuwar masarautarsa.
An gina sabuwar masarautar a Oke Aremu da ke karamar hukumar Ibadan ta Arewa da ke jihar Oyo a Najeriya, cewar Daily Post.
Oyo: Fitar karshe da basaraken ya yi
Sai dai bai samu halartar nadin sarautar basarake mai daraja Olubadan ba a matsayin na 43 da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yulin 2024.
Rahotanni sun tabbatar da cewa bude masarautar da aka gudanar ita ce fitarsa ta karshe a hukumance har zuwa lokacin mutuwarsa.
An kwantar da marigayin a gadon asibiti tun ranar 13 ga watan Yulin 2024 har zuwa yau kafin ya ce ga garinku.
Gwamna Makinde ya magantu kan dokar masarautu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Oyo ta yi karin haske kan gyaran fuska game da masarautun jihar da ake ta zarge-zarge a kansu.
Gwamnatin jihar ta musanta zargin da ake yadawa cewa ta dauki matakin ne domin hana gadon kujerar Olubadan.
Hakan na zuwa ne bayan yada jita-jitar a lokacin bikin nadin sarautar sabon sarkin Ibadan da ake kira Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin.
Asali: Legit.ng