Dangote: Kwankwaso Ya Dauki Zafi Kan Rigimar, Ya Gargadi Gwamnatin Tinubu

Dangote: Kwankwaso Ya Dauki Zafi Kan Rigimar, Ya Gargadi Gwamnatin Tinubu

  • Yayin da ake ta rigima kan matatar Aliko Dangote, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ba gwamnatin Bola Tinubu shawara
  • Kwankwaso ya ce abin takaici ne yadda ake ta ce-ce-ku-ce kan sahihancin matatar inda ya ce kamfanin na bukatar hadin kai
  • Hakan ya biyo bayan rigima tsakanin Aliko Dangote da kuma hukumar NMDPRA kan sahihancin man da matatar ke fitarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jagoran siyasar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi martani kan rigimar Aliko Dangote da hukumar NMDPRA.

Kwankwaso ya gargadi Gwamnatin Tarayya inda ya ce ya kamata ta yi mai yiwuwa domin tabbatar da inganta matatar Dangote.

Kwankwaso ya yi magana kan rigima da ake yi game da matatar Dangote
Sanata Rabiu Kwankwaso ya shawarci gwamnatin Tinubu kan mutunta matatar Aliko Dangote. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Kwankwaso ya tsoma baki a rigimarsu Dangote

Kara karanta wannan

An samu baraka tsakanin Kwankwaso da gwamnatin Kano? Gaskiyar magana ta fito

Jigon NNPP ya bayyana haka ne a yau Laraba 24 ga watan Yulin 2024 a shafinsa na X inda ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kwankwaso ya bayyana kokwanto kan sahihancin matatar da shiririta inda ya bukaci gwamnatin Tinubu ta yi adalci dangane da matatar.

"Na samu damar kai ziyara matatar Dangote inda na yi mamakin ganin yadda aka inganta matatar."
"Wannan matatar tana da muhimmanci wurin samar da makamashi da kuma inganta tattalin arziki wanda dole a bata dukkan kariya daga masu barazana."
"Abin takaici ne yadda ake ta korafi kan sahihancin matatar wanda hakan zai lalata kokarin samar da ita da kashe guiwar masu zuba hannun jari."

- Rabiu Kwankwaso

Dangote: Kwankwaso ya ba Bola Tinubu shawara

Sanata Kwankwaso ya ce ya kamata a ba matatar Aliko Dangote dukkan goyon bayan domin tabbatar da cigabanta ba tare da ta samun matsala ba.

Kara karanta wannan

Shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fadi illar 'bita da kulli' ga matatar dangote

Ya ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta ba da dukkan goyon baya da kwarin guiwa ga wannan aiki mai muhimmanci.

Kotu ta zauna kan shari'ar Kwankwaso, EFCC

Kun ji cewa an samu matsala a shari'ar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shigar da hukumar EFCC kara kan take hakkinsu na 'yan kasa.

An samu matsala ne bayan EFCC ta gaza shiryawa kan karar da Sanatan da wasu mutane bakwai suka shigar a gaban Babbar Kotun jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.