Tinubu: Fitaccen Sarki Ya Aika Muhimmin Saƙo ga Matasa Masu Shirin Yin Zanga Zanga

Tinubu: Fitaccen Sarki Ya Aika Muhimmin Saƙo ga Matasa Masu Shirin Yin Zanga Zanga

  • Sarkin Benin, Oba Ewaure II ya yi kira ga matasan Najeriya su janye zanga-zangar da suka shirya yi ranar 1 ga watan Agusta, 2024
  • Basaraken ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsaren da ake sa ran za su share hawayen ƴan Najeriya
  • Matasa dai sun tsara fita zanga-zanga kan kuncin rayuwa da rashin tsaro a wata mai kamawa kuma sun ce za su ɗauki kwanaki 10 suna yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Oba na Benin da ke jihar Edo, Oba Ewaure II ya yi kira ga matasan Najeriya su janye zanga-zangar da suka shirya farawa daga ranar 1 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, tsohon kakakin kamfen Atiku ya fice daga PDP zuwa APC

Fitaccen sarkin mai daraja ta ɗaya ya yi wannan kira ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Osaigbovo Iguobaro, ya fitar ranar Laraba.

Oba na Benin, Oba Ewaure II.
Oba na Benin ya bukaci matasa su karawa shugaban kasa Bola Tinubu lokaci Hoto
Asali: Twitter

Basaraken ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ba gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu isasshen lokaci domin aiwatar da tsare-tsaren da ta zo da su na tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ana sa ran tsare tsare za su kawar da wahalhalun da ƴan Najeriya ke kuka da su a yanzu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Kafin abubuwa da zauna daidai sai an ɗan sha wuya ta ɗan kanianin lokaci," in ji Oba na Benin.

Oba ya aikawa Bola Tinubu sako

Har ila yau Sarkin ya waiwaya kan gwamnatin tarayya, inda ya yi kira da ta ƙara ƙaimi wajen aiwatar da manufofinta na tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana dalilin da ya sa ba ta son a yi zanga zanga

Idan ba ku manta ba matasan Najeriya sun shirya fita zanga-zangar kwanaki 10 da suka tsara farawa ranar 1 ga watan Agusta, 2024 a faɗin ƙasar nan.

Fusatattun matasan sun ce sun ɗauki wannan matakin ne domin jawo hankalin gwamnatin tarayya game da kuncin rayuwar da ake ciki.

Shugaba Tinubu ya nemi karin lokaci

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya roki matasan su ƙara masa lokaci domin ya magance duk abubuwan da suka zame masu damuwa.

Sakamakon haka ne sarkin Benin, Oba Ewuare ya shawarci wadanda ke shirin gudanar da zanga-zangar a fadin kasar su haƙura su janye, rahoton The Nation.

Tinubu ya yi wa jihohi 34 yayyafin N438bn

A wani rahoton kuma, an ji Gwamnatin Bola Tinubu ta saki kudi har N438b ga jihohi 34 da babban birnin tarayya domin rage matsin tattalin arziki.

Ta ware kudin ne a karkashin shirin NG-CARES wanda ta ce ta tantance jihohin a watan Janairu kuma ta saki kudin kwanan nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi hanyar magance zanga zangar da ake shirin yi

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262