Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa Ba ta Son a Yi Zanga Zanga

Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa Ba ta Son a Yi Zanga Zanga

  • Gwamnatin taraya ta bayyana dalilin da ya sa ba ta so matasa su fito su gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ya ce ba son ayi zanga-zanga ne saboda ba a cika gamawa lafiya ba
  • Mohammed Idris ya bayyana cewa akwai baragurbi masu jira a fara zanga-zanga su yi kutse domin tayar da rikici

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana dalilin da ya sanya ba ta so a gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Mohammed Idris, ya ce ko kaɗan gwamnatin ba ta so matasa su fito kan tituna domin yin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Tinubu: Fitaccen Sarki ya aika muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

Gwamnatin tarayya bata son a yi zanga-zanga
Gwamnatin Tinubu bata son matasa su yi zanga-zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bata-gari za su bata zanga-zanga?

Mohammed Idris ya ce yayin da ƴan Najeriya ke da ƴancin gudanar da zanga-zanga, gwamnati na sane da cewa wasu mutane na shirin yin kutse domin tayar da rikici, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ƴan tawagar Charismatic Bishop Conference yayin wata ziyara da suka kai masa a ofis ɗinsa ranar Laraba a Abuja.

Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yarda da cewa kowane ɗan Najeriya na da ƴancin yin zanga-zanga.

A cewarsa, gwamnati ta duƙufa wajen ganin cewa zanga-zangar ba ta kawo cikas ga zaman lafiya ba ko take haƙƙin wasu.

Zanga-zanga: Jawabin gwamnatin Tinubu a yau

"Shugaban ƙasa ba ya adawa da yin kowace irin zanga-zanga amma yana adawa da yin rikici da duk wani abu da zai kawo cikas ga jin daɗin ƴan Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi hanyar magance zanga zangar da ake shirin yi

"Dalilin da ya sanya kowa yake taka tsan-tsan da wannan zanga-zangar shi ne saboda abin da muka ga ya faru a wasu sassan duniya."
"Mun san cewa abu ne mai matuƙar wahala a yi zanga-zanga sannan daga ƙarshe a samu zaman lafiya. Hakan ba zai yiwu ba saboda wasu mutane na jira su ɗauki doka a hannunsu."

- Mohammed Idris

Gwamnati na so a fasa zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan saboda matsalar karancin abinci da yunwa, da su kwantar da hankalinsu.

Gwamnatin ta buƙace su da su rungumi zaman lafiya, tana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da ministocinsa na ƙoƙarin sauya lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng