Gwamna Ya Jinjina, Tinubu Ya Kafa Tarihi a Arewa Maso Yamma Cikin Watanni 14 a Mulki
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya mika sakon godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan gagarumin aiki da zai kawo a Arewa
- Uba Sani ya bayyana irin farin ciki da yayi bayan Bola Tinubu ya sanya hannu a kan kudurin dokar samar da hukumar Arewa ta yamma
- A jiya Talata ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar samar da hukumar cigaban jihohin da ke Arewa maso yamma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shan yabo bayan kafa hukumar cigaban Arewa maso yamma.
Gwamna Uba Sani ya mika godiya ga shugaban kasa Bola Tinubu bisa kokarin da ya yi na kafa hukumar.
Legit ta gano bayanin da Uba Sani ya yi ne a cikin wani sako jami'in yada labaran gwamnatin Kaduna, Muhammad Lawal Shehu ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NWDC: Gwamna Uba Sani ya godewa Tinubu
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya mika sako na musamman ga Bola Tinubu kan samar da hukumar cigaban Arewa maso yamma (NWDC).
Uba Sani ya ce samar da hukumar NWDC na cikin abubuwan masu muhimmanci da suka faranta masa rai cikin shekaru sama da 10 da suka wuce.
Daily Trust ta ce Uba Sani ya kara da cewa samar da hukumar na cikin abin da zai nuna cewa Bola Tinubu ya bayar da muhimmanci ga Arewa maso yamma.
Amfanin NWDC ga Arewa maso yamma
An kafa hukumar NWDC ne domin kawo cigaba da bunkasa jihohi bakwai da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya.
Saboda haka ne ma gwamna Uba Sani ya ce hukumar za ta taimaka wajen share hawayen jihohin musamman ta bangaren tsaro da haɓaka tattali.
Uba Sani ya bayyana cewa dole za su kawo tsari da zai kawo cigaba ga dukkan al'ummar yankin ba tare da nuna wariya ga kowa ba.
Uba Sani ya koka kan El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa Uba Sani ya yi Allah wadai da irin mummunan halin da ya tsinci manyan asibitoci da ake da su a jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna ya ce an yi shekaru 20 ba a gyara asibitocin ba, amma ya dauki alkawarin zai gyara matsalolin cikin gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng