NNPCL: Kalaman Ɗangote Sun Tada Ƙura, Tsohuwar Minista Ta Aika Saƙo Ga Bola Tinubu

NNPCL: Kalaman Ɗangote Sun Tada Ƙura, Tsohuwar Minista Ta Aika Saƙo Ga Bola Tinubu

  • Yayin da aka fara musayar yawu tsakanin NNPC da Aliko Ɗangote, tsohuwar ministan ilimi, Oby Ezekwesili ta buƙaci a yi bincike
  • Madam Ezekwesili ta yi zargin cewa maganganun da ke ƙara bayyana sun nuna cewa akwai wani abin a ƙasa da ya kamata a tono
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban NNPCL, Mele Kyari ya musanta zargin cewa yana da kamfanin tace danyen mai a kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan abubuwan da ke faruwa tsakanin NNPCL da matatar Ɗangote.

Ezekwesili ta bukaci a yi bincike don gano dalilin da ya sa kamfanin mai na ƙasa ya ƙayyade zuba jari a matatar Ɗangote a ƙaso 7.2% maimakon 20% da aka tsara a baya.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya 'lakadawa' wata mata dukan tsiya a Kano, an samu bayanai

Oby Ezekwesili da Bola Tinubu.
Oby Ezekwesili ta buƙaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan rikicin NNPCL da matatar Ɗangote Hoto: Oby Ezekwesili, Ajuri Ngelale
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne bayan shugaban NNPCL, Mele Kyale ya musanta zargin cewa yana sarrafa wata masana'antar mai a ƙasar waje, Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nesanta kansa da mallakar masana'antar ne yayin da yake martani ga ikirarin Aliko Ɗangote, wanda ya yi zargin cewa wasu jami'an NNPCL suna da kamfanin mai a Malta.

Misis Ezekwesili ta tsoka baki a batun

Da take martani kan rikicin Ɗangote da NNPCL, taohuwar ministar ta ce da farko ta yanke tsame hannunta kan abubuwan da ke faruwa, Guardian ta tattaro.

"Ganin yadda bayanai ke ƙara fitowa, dole mu yi tunanin akwai wata a ƙasa kuma da buƙatar a fayyace komai don al'umma su sani," in ji ta.

Misis Ezekwesili ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa a yi bincike mai zaman kansa kan mu'amalar NNPCL da matatar Ɗangote domin al'umma su san haƙiƙanin abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

N70,000: Ƴan aikin gida za su sha romo, majalisa da ƙungiyar NCWS sun miƙa bukata

"Taya aikin matatar man da ta ja hankalin duniya za a nemi gurɓata shi a wani rikici mara ma'ana.
"Shin ba gwamnatin Najeriya ce ta fito ta gaya mana cewa ta ciyo bashin dala biliyan 3.3 daga bankin Afriexim-Bank domin zuba hannun jari a matatar man Dangote ba?"

Tinubu ware wa tituna N2trn

A wani rahoton kuma babban titin Legas zuwa Kalaba da wasu manyan tituna a faɗin ƙasar nan za su laƙume kusan N2trn daga ƙarin kasafin kudin 2024

Majalisar tarayya ta amince da kudirin ƙara N6.2trn a kasafin kuɗin kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262