Yan Hisbah Sun Shiga Matsala Bayan Mutuwar Mutum a Wajen Bikin da Suka Kai Samame

Yan Hisbah Sun Shiga Matsala Bayan Mutuwar Mutum a Wajen Bikin da Suka Kai Samame

  • Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Farouq Lawal Jobe ya kafa kwamiti domin binciken hukumar Hisbah kan zargin kisan kai
  • Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari ya yi karin haske kan zargin da ake yi wa hukumar Hisbah da binciken da ake yi
  • Ana zargin hukumar Hisba ne da laifin kisan kai da muzgunawa al'umma a lokacin wani biki da ya gudana a baya a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta kafa kwamiti domin yin bincike kan zargin da ake yiwa wasu jami'an hukumar Hisbah.

Ana zargin jami'an hukumar Hisbah ne a Katsina da kisan kai yayin wani taron biki da ya gudana a jihar.

Kara karanta wannan

An tona yadda bata gari ke shirin kai hari gidan gwamnati da sunan zanga zanga

Gwamna radda
Za a binciki yan Hisbah bisa zargin kisan kai a Katsina. Hoto: Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe ne ya kafa kwamitin domin bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe Gambo mai faci

Rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar Hisbah a Katsina sun kai samame ne a yayin wani gagarumin biki.

An ce da isar yan Hisbah wurin bikin suka fara harbi sama wanda hakan ya jawo mutuwar wani mutum mai suna Gambo mai sana'ar faci.

Gwamnati za ta binciki hukumar Hisbah

Biyo bayan kisan Gambo mai faci, mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Faruk Umar ya kafa kwamiti domin bincike kan lamarin.

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa za a binciki yadda aka kashe Gambo mai faci ne da kuma yadda aka muzgunawa mutane yayin hidimar bikin.

Yaushe za a kammala binciken Hisbah?

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Faskari ya ce nan da kwanaki 10 kwamitin zai kammala bincike.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kai aikin da zai taimaka kan dakile matsalar tsaro a mahaifar shugaba Buhari

Kwamishinan matasa da wasanni ne zai jagoranci kwamitin sai kuma sakataren dindindin na ma'ikatar addini da sauransu da za su taimaka masa.

An kafa dokar idda a jihar Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Malam Dikko Radda ta kafa dokar bai wa matan da mazansu suka rasu hutun iddah.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban ma'aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ya ce tuni aka tura sanarwa ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng