Sakataren Gwamnati Ya Sa Labule da Ministocin Tinubu Kan Zanga Zanga, Bayanai Sun Fito

Sakataren Gwamnati Ya Sa Labule da Ministocin Tinubu Kan Zanga Zanga, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin tarayya ta tashi tsaye a kokarin daƙile yunkurin da matasa ke yi na hawa kan tituna a watan Agustan nan mai zuwa
  • Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya shiga taron gaggawa da Nuhu Ribadu da ministocin kasa kan batun zanga-zanga
  • Bola Tinubu ya roƙi masu shirya wannan zanga-zanga su kara hakuri domin kokensu ya isa gare shi kuma zai magance su nan kusa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume ya sa labule yanzu haka da ministoci kan zanga-zangar da matasa ke shirin yi a faɗin ƙasar nan.

Bayanai sun nuna cewa taron wanda ke gudana cikin sirri, ya samu halartar kusan duka ministocin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

An kashe mutane yayin da rigimar sarauta ta ƙara tsanani, hadimin gwamna ya yi magana

George Akume da Nuhu Ribadu.
George Akume da Nuhu Ribadu sun shiga taron gaggawa da ministoci kan zanga-zanga Hoto: George Akume, Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Haka nan kuma mai bai shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu na cikin mahalarta taron a Aso Villa, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan Najeriya na shirin yin zanga-zanga

The Nation ta ruwaito cewa wasu ƴan Najeriya karƙashin kungiyoyi daban-daban galibi matasa sun shirya zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.

Masu shirya zanga zangar sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da ake ciki.

Wannan lamari dai ya sa dakarun ƴan sanda da sauran jami'an tsaro zama cikin shiri kan wannan gagarumar zanga-zanga da ake shirin yi.

Idan ba ku manta ba, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roƙi masu shirin yin zanga-zanga su haƙura sun janye kana su ƙara masa lokaci don magance kokensu.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya dauki zafi kan zanga zanga, ya fadi dalilin shiryata

Gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye kan batun

Wasu daga cikin ministocin da aka ga zuwansu sun haɗa da Nyesom Wike (Abuja), Yusuf Tuggar (ma’aikatar harkokin waje) da Zephaniah Jisalo (Ayyuka na musamman).

A taron akwai Tahir Mamman (Ilimi) da Abubakar Bagudu (ƙasafi da tsare-tsare).

Sauran su ne Wale Edun (Kudi), Mohammed Idris (yaɗa labaraii), Bello Matawalle (tsaro), David Umahi (ma'aikatar ayyuka) da dai sauransu.

Atiku ya caccaki Tinubu kan zanga-zanga

A wani rahoton kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa masu son tauye ƴancin yin zanga-zanga a yanzu, su ma sun jagoranceta a shekarar 2012 a mulkin Goodluck Jonathan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262