Kungiyar Kwadago Ta Janye Shiga Zanga Zangar Adawa da Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana
- Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta musanta cewa ta janye daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan
- Ƙungiyar ta ce ba ita ta shirya zanga-zangar ranar, 1 ga watan Agusta ba, saboda haka ba yadda za ayi ta iya janyewa daga cikinta
- Shugaban ƙungiyar ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya kira masu zanga-zanga su zauna domin jin buƙatunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC) ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ta janye daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar, 1 ga watan Agusta a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar NLC ta musanta janyewa daga zanga-zangar da za a shirya domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Martanin ƙungiyar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X, a ranar Laraba, 24 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me NLC ta ce kan janyewa zanga-zanga?
A cikin sanarwar shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce ƙungiyar ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ita ta shirya ba.
"Mun lura da rahoton da ke cewa ƙungiyar ƙwadago ta fice daga zanga-zangar ƙasa da ake ta tattaunawa a kai. NLC ta musanta wannan labari a matsayin ƙarya tsagwaronta."
"Maganar gaskiya ita ce ƙungiyar ƙwadago ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar da ba ita ta shirya ba. Wadanda suka shirya zanga-zangar ne kawai za su iya yanke shawarar janyewa ko ci gaba da zanga-zangar."
- Joe Ajaero
Kungiyar NLC ta ba Tinubu shawara
Ajaero ya kuma yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gayyaci jagororin zanga-zangar domin tattaunawa da su kan buƙatunsu.
Ya nemi gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da su saurari koke-koken al’ummar Nijeriya, su yi abin da ya kamata.
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Ministan Tinubu ya dauki zafi kan zanga zanga, ya fadi dalilin shiryata
- Atiku ya yi magana kan zanga zanga, ya aika sako mai zafi ga Tinubu
- APC ta fallasa masu shirya zanga zangar adawa da gwamnatin Tinubu
Gwamnatin Tinubu ta zaftare alawus
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da rage alawus-alawus da ake ba ƴan Najeriya da ke karatu a ƙasashen waje.
Ɗaliban su na karatu ne ƙarƙashin tsarin bada tallafin karatu tsakanin Najeriya da ƙasashen waje a ƙasashen Morocco, Rasha da Algeria da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng