Kashim Shettima ya Kaddamar da Manyan Ayyuka a Jigawa, an Raba Kyautar Kudi
- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ayyukan ci gaban jama'a a jihar Jigawa, wanda mataimakin shugaban kasa ya jagoranta
- Yayin kaddamar da daya daga cikin ayyukan taron masu kanana da matsakaitan sana'o'i, Sanata Kashim Shettima ya raba kyautar kudi
- Ya kuma kara gaba inda ya kaddamar da gonar noman rani mai girman kadada 10 tare da wasu shagunan sauki a sassan jihar Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da manyan ayyukan bunkasa rayuwar talakawa da raya kasa a jihar Jigawa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya kaddamar da aikin a ranar Talata, inda ya kaddamar da wasu ayyukan bunkasa noma.
Sanata Kashim Shettima, ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya lissafa manyan ayyukan da ya kaddamar da su ka hada da raba tallafin kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigawa: Ayyukan da Kashim Shettima ya kaddamar
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da wasu manyan ayyuka guda hudu a sassan jihar Jigawa, wadanda su ka hada da;
1. Kaddamar da rabon tallafi
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar rabon tallafi ga masu kanana da matsakaitan sana'o'i (MSME) a jihar Jigawa, Jaridar Vanguard ta wallafa.
Ya raba tallafin yayin bude taron kananan 'yan kasuwa karo na hudu da gwamnatin tarayya ke yi a fadin kasar nan, inda ya mika kyautar N150,000 ga kowanne mai karamar sana'a.
Sanata Kashim ya kara da cewa masu kananan sana'o'i na da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar nan, domin su ne 95% na sana'o'in kasar nan.
An kaddamar da irin wannan a jihohin Binuwai, Ogun da Ekiti.
2. Kaddamar da shagunan sauki
Daga raba tallafi ga masu kananan sana'o'i, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da shagunan sauki da aka yi wa lakabi da 'Solar Kiosks.'
An samar da shagunan ne domin saukaka farashin kayan masarufi ga mazauna jihar Jigawa a dukkanin kananan hukumomin jihar.
3. Kaddamar da gonar noman rani
Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da wata gona da ke kauyen Sumore mai aiki da hasken wutar rana.
Mataimakin shugaban kasar ya kaddamar da gonar mai kadada 10 inda ake noma kayan lambu kuma a gefe guda ake noman ranin shinkafa.
Gwamnati za ta kaddamar da raba tallafi
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa za ta raba kayan amfanin noma ga manoma 30 a jihar domin habaka samar da abinci.
Kwamishinan yada labarai, wasanni, al'adu da mata, Sagir Musa ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa majalisar zartaswar jihar ta amince da fitar da Naira biliyan 3.5 domin yin rabon.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng