An Kashe Mutane Yayin da Rigimar Sarauta Ta Ƙara Tsanani, Hadimin Gwamna Ya Yi Magana
- Mutum biyu sun rasa rayuwarsu yayin da rikicin sarauta ya ƙara tsananta a Araromi-Owu, ƙaramar hukumar Ayedaade a Osun
- Mazauna garin sun bayyana cewa rigimar ta fara ne tun a makon jiya daga bisani ta rikiɗe ta zama tashin hankali ranar Talata
- Gwamnatin jihar Osun ta musanta ikirarin wasu majiyoyi, ta ce mutum biyu ne kaɗai suka rasa ransu a rikicin nan da ya barke
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Ana fargabar kashe mutane biyu a rikicin da ya barke kan sarauta a garin Araromi-Owu da je karamar hukumar Ayedaade a jihar Osun.
Bayanai sun nun cewa rikicin wanda ya faro tun makon jiya ya ƙara dagulewa a ranar Talata, 23 ga watan Yuli, 2024.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa dambarwar ta ƙara ƙamari a jiya Talata wanda sai da ta kai ga wasu ɓangare suka fara ƙone-ƙonen motoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rikicin sarautar ya ƙara muni
Wani mazaunun yankin, Ismail Olaoye ya bayyana cewa wasu ƴan daba da ɓangare ɗaya daga cikin masu rigimar sarautar suka ɗauko haya sun ƙara ta'azzara lamarin.
A cewarsa, ƴan daban sun cinna wuta a kan titin shiga garin domin hana jami'an tsaro kawo ɗauki da nufin kwantar da tarzoma.
Haka nan kuma wasu ɓata gari sun yiwa jami'an tsaron da aka turo kwantan ɓauna, inda suka raunata wasu daga ciki.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutum biyar ƴan daban suka kashe a rikicin tare da ƙona gidaje da motoci.
"Bangaren da suka ɗauki zafi sun yi ikirarin cewa sarautar tasu ce bayan an naɗa wani daban, hakan ya haifar da zanga-zanga tsawon kwanaki daga bisani ta rikiɗa ta koma rikici," in ji shi.
Osun: Wane mataki mahukunta suka ɗauka
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola ya ce an tura dakaru na musamman zuwa garin domin dawo da zaman lafiya.
A nasa jawabin mai baiwa gwamnan Osun shawara kan harkokin tsaro, Barista Samuel Ojo, ya ce mutum biyu aka kashe a rikicin ba biyar ba kamar yadda wasu majiyoyi suka yi ikirari.
Samuel Ojo ya ƙara cewa ba dan gwamnati ta shiga tsakani ba da rikicin ya fi haka muni, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Malami ya nemi gwamna ya tsige sarki
A wani rahoton kun ji cewa an bukaci gwamnan Osun, Ademola Adeleke da ya tuge sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi daga sarautar garin
Malamin addinin gargadiya, Satguru Maharaj Ji shi ya bukaci hakan daga gwamnan saboda yadda sarkin ke zubarwa masarauta mutunci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng