Gwamnatin Tarayya Ta Zaftare Alawus Din 'Yan Najeriya da Ke Karatu a Waje, Ta Bayyana Dalili

Gwamnatin Tarayya Ta Zaftare Alawus Din 'Yan Najeriya da Ke Karatu a Waje, Ta Bayyana Dalili

  • Gwamnatin tarayya ta zaftare kuɗaɗen alawus da take ba ɗaliban Najeriya da ke karatu a ƙasashen waje daga $5,650 zuwa $4,370
  • Ɗaliban dai suna karatu a ƙarƙashin shirin ba da tallafin karatun da Najeriya ta ƙulla yarjejeniya tsakaninta da wasu ƙasashen waje
  • Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin tsuke aljihunta ne saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage alawus-alawus da ake ba ƴan Najeriya da ke karatu a ƙasashen waje.

Ɗaliban suna karatu ne ƙarƙashin tsarin bada tallafin karatu tsakanin Najeriya da ƙasashen waje a ƙasashen Morocco, Rasha da Algeria da sauran wasu ƙasashe.

Kara karanta wannan

An kashe mutane yayin da rigimar sarauta ta ƙara tsanani, hadimin gwamna ya yi magana

Gwamnatin tarayya ta zaftare alawus din malamai
Gwamnati ta rage alawus din da take ba 'yan Najeriya da ke karatu a kasashen waje Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnati ta zaftare alawus ɗin ɗalibai

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan watan ranar 23 ga watan Yuli, 2024, wacce hukumar ba da tallafin karatu ta tarayya ta aika ga ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasiƙar an rage alawus ɗin wata-wata daga $500 zuwa $220, alawus ɗin kammala karatu daga $2500 zuwa $2000, da alawus ɗin yin bincike na PG daga $1,000 zuwa $500.

Rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da labarin nan a tsakiyar makon nan.

Kudin da gwamnati ta ke biya ya ragu

Jimillar alawus ɗin da ake biya a baya $5,650 ne kan kowane ɗalibi, amma yanzu an zaftare shi ya koma $4,370.

Sai dai, zaftarewar ba ta shafi alawus ɗin inshorar lafiya, kuɗin jirgi da kuɗin magani wanda har yanzu suke a matsayin $200, $700, $500 kamar yadda suke a baya.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin rattaba hannu kan kudirin dokar mafi karancin albashi

Meyasa gwamnati ta rage kuɗaɗen?

Wasiƙar ta bayyana cewa an rage kuɗaden ne saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki a ƙasar nan.

An kuma yi musu alƙawarin biyansu kuɗadensu na shekarar 2023 da 2024 da suka biyo da zarar kuɗaɗen sun samu.

Rahotanni dai na cewa daliban sun kwashe wajen watanni takwas ba tare da biyansu kuɗaɗen alawus ɗin ba.

Batun siyar da jami'o'in Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan jita jitar cewa za ta sayar da jami'o'in Najeriya ga turawa.

Ministan ilmi, Farfesa Tahir Mamman wanda ya yi wannan ƙarin hasken ya tabbatar da cewa babu ƙamshin gaskiya a zancen ƙanzon ƙuregen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng