Tinubu Na Shirin Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Mafi Karancin Albashi

Tinubu Na Shirin Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Mafi Karancin Albashi

  • Ƙudirin dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kusa zama doka inda yanzu yake jiran sanya hannun shugaban ƙasa
  • Ƙudirin ya samu amincewar majalisar dattawa da majalisae wakilai bayan an gabatar da shi a gabansu a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024
  • Za a miƙa sabon kwafi na ƙudirin ga Shugaba Bola Tinubu domin ya rattaɓa hannunsa a kai ya zama doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu takardar sabon ƙudirin mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya.

Shugaban ƙasan zai samu kwafin ƙudirin ne domin amincewa da shi bayan majalisar tarayya ta amince da shi a jiya Talata, 23 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki mataki kan kudirin sabon mafi karancin albashi da Tinubu ya mika

Tinubu zai sa hannu kan kudirin dokar mafi karancin albashi
Kudirin dokar mafi karancin albashi na jiran sa hannun Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Majalisu sun amince a biya ma'aikata N70,000

Majalisar dattawa da majalisar wakilai duka sun amince da ƙudirin bayan an gabatar da shi a gabansu, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin majalisun ne suka karanta ƙudirin wanda ya ƙayyade N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da wa'adin shekara uku domin sake yin waiwaye kan mafi ƙarancin albashin.

Majalisun biyu ba su ɓata lokaci ba wajen amincewa da ƙudirin sabon mafi ƙarancin albashin wanda ya samu karatu na ɗaya zuwa na uku kafin a amince da shi ba, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Tinubu ya miƙa ƙudiri gaban majalisu

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar da ƙudirin ne a gaban majalisun ta hanyar wata wasiƙa da ya aike musu.

Ƙudirin ya sanya mafi ƙarancin albashin N70,000 ya zama doka wanda aka amince da shi tsakanin ƴan ƙwadago, kamfanoni masu zaman kansu da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Ƙudirin ya kuma rage yawan shekarun da ake yin waiwaye kan mafi ƙarancin albashin daga shekara biyar zuwa shekara uku kamar yadda Shugaba Tinubu ya yi alƙawari yayin zamansa da shugabannin ƴan ƙwadago.

Gwamnan Benue zai biya N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta biya ma'aikatan jihar N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai ranar Jumu'a, 19 ga watan Yuli, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng